Bude idonta keda wuya me zataji? Karan motoci sun tsaya. Ta cire niqab ta kalla inda take ta hango window, ta rarrafa ta dan leka don taga kosu waye. Kirjinta ya bada damm da taga kosu waye. Tabdi! Wai ta yaya suke sanin inda takene? Tayi gudu tayi gudu amma inaaa, mutane kaman sunsa mata tracker.
"Ku duba gidajen nan daya bayan daya, karku ketare ko daya, saikun nemota, MAZA!"
Sojoji sanyeda mask(takunkumin fuska) suka rarrabu zuwa gidajen wurin. Sergeant yana tsaye, sagale da bindigarshi a baya, hannayenshin kan kugu ya gama bada oda, gefenshi doctor ne sanye da farin hazmat suit, a bayanshi crew dinshine suma sanye da suit din su uku.
Matar mansoor tayi sauri ta noke ta makale da bango tana tunanin mafita. Tunda ta fara gudunsu suke cimmata, sun dai rantse sai sunsha jininta, mayu kawai. Ahir dinsu don wallahi sai inda karfinta ya kare.
* * * *
Bayan matar mansoor tayi gudu harta ga kanta cikin wani gida, batasan yanda akeyi tazoba, gajiya ya bade jikinta ta zube jikin bango, idanunta sunyi nauyi se bacci.
Farkawa tayi taji wani irin kara kaman dodo, ah ah! Wane dabbane anan yake kuka hak.....kurururur kwaaaa. Ta kalla cikinta, tooo, ashe shine? Ta shafa cikin tana kallon inda take. Gidan ba kowa kuma ko'ina bude yake. Kila mutanen gidan sun gudu ne lokacin rudanin CD, suka watse ko suka mutu.
Ta dudduba kicin tana neman abinci, ta samu biredi mai hunhuna, kayan miya sunyi hunhuna, ta bude pampo ruwa ya zubo. Cikin zumudi ta daga niqab ta tara hannayenta tayita kwankwada harya isheta. Ta cigabada neman abinci, bude cupboard keda wuya taga indomie super pack, haba tayi kaca kaca da ledan ta dinga dumbuzawa a baki karas karas tayita ci.
Kara taji na motoci sun tsaya mutane nata surutu. Da sauri ta leka ta windo taga sojoji da likitoci, aiko tayi sauri ta bar gidan cikin nasara don ta baya tabi kuma babu kowa ta wurin. Shine farkon haduwanta dasu. Da sojoji kawai ta gani bazata damu ba sosai don sunata yawo a garin tun faruwar barkewan annoban, amma likitoci? Anya ba daga wurinnan bane suka biyota? Wurin killace mutane nan?
Amma wadannan mutane akwai jaraba, inde ita suka biyo. Yama suka san inda take? Tayita sauri sauri gudu gudu, can dai taji kaman suna shiga motocinsu ta harba a guje ta dauka wata hanya. Isowanta wani layi taga chemist makale da wani gida.....tsaya, wannan ai gidantane.
Cikin hanzari ta shige, lallai shine to amma ya akeyi bata gane nata gidanba? Ta yarda hankali ke gani ba idanuba. Ta kalla tsakar gidan inda mijinta mansoor ya fadi ya mutu, shekenan bazata sake ganinshiba har abada. Allah sarki, mansoor mijine mai sonta, yana bata kula kuma yanada kirki, ga tsoron Allah dabin doka kowace irice inde mai kyauce. To dama haka rayuwa take, gashi yanzu ita kadaice a wannan gari daya shiga rudani.
Shiganta keda wuya zata cire niqab ta sankare, karan motoci kuma, ta saurara taji dai lallai layin suka shigo. Ta lallaba ta fita tabi bayan gidanta ta ruga a guje. Kasuwa ta fada wannan karon kaman anyi sharan jama'a an tarasu a wurin. Gawawwakine a tule, wani kan wani. Ta wucesu ta shiga shagon kayan abinci, ta dauka leda ta tula su indomie, biskit, dasu juices da ruwa.
Fita daga shagon keda wuya taci karoda soja amma ya bata baya. Ta taka birki ta waiwaiga ta fara jada baya kawai saiya waigo. Haba, kafa me naci ban bakiba fittt ta bar wurin cikin walkiya. Mamaki ya kama sojan amma ya bita a guje yana magana ta ear piece din kunnenshi.
"Falcon hadari, naga matar a kasuwan dandano amma ta gudu, am in pursuit now but she's out of view...".
Gudu take kaman ba gobe, ledanma data cika da kaya batasan inda suka zubeba, hala acan tabarshi wurin sojan. Hannunta rike yake kawai da roban ruwa. Gaskiya mutanen nan sun addabeta, wai jinintane kadai keda abinda suke nema da zasu ta binta ba taka birki?
Sergeant yana zaune cikin mota a seat din gaba motar na tafiya, ya dafa kunne ya gama sauraren magana. "Mobilizing all FH(falcon hadari) team, retreat to kasuwan dandano and its neighborhoods, find her, do not let her escape".
* * * *
To yanzu karfin nata ya kare kenan? Ta gaji da gudu kaman gada wallahi. Inta amince suka kamata batasan me zasuyi da itaba, aiko gwara tayi ta kanta. Da kyar ta mike rikeda niqab, ta lallaba tayita bin kusurwa harta fice daga gidan tana boye boye har Allah yasa ta bar wurin kaman wata aljana, babu wanda ya ganta har tayi nisa ta kara wuta.
Tuntuni yake ta kallon su daga balcony na gidanshi sunata abu daya su biyu, da budurwa da yarinya, kallon wasu likitoci masu gwaje gwaje sunsa suit na kariya daga cututtuka sunata daukan jinin gawawwaki, hardai sababbin. Tareda likitocin akwai sojoji sunsha gas mask tsaye da bindigoginsu rike a hannayensu. Su budurwar suna labe sunata kallon likitocin, shi kuma abu yana saman balcony yana lekensu ta karafen dake tare faduwa daga balcony zuwa mutuwa. Amma basu hango shiba saboda tabarmar kwakwa ta rufe karafen. Shikuma yana ganinsu ta inda tabarmar ta bule.
Likitocin na gama kwasan samples suka shiga motocinsu tareda sojojin suka wuce. Abu ya maida hankalinshi gun budurwar da yarinyan kwatsam sai yaga idanunsu kyar a inda yake. Kirjinshi ta bada damm badai sun ganshiba? To amma ai bazasu iya ganinshiba saboda tabarmar.
Me zai gani? Suna tahowa inda yake. Infa sukazo suka bade shida CD? Da sauri ya mike tsaye ya leko ta saman karafen yagansu a kasa, a gaban gidanshi. "Ku tsaya nan karku karaso."
Suka daga kai sunata kallonshi ba magana. To lafiya suketa kallonshi? Abu ya kalla kayansu dukun dukun kawai saiyaga sun cigabada shiga gidan. Daman bai kulle kofan kasaba yanzu zasu iya shigowa tsakar gidan amma ya kulle palonshi dake kasa.
Da gudu ya sulalo kasa daga stairs din cikin gidan ya iso kofar palo ya daga labule, kawai ganinsu yayi tsaye suna jiranshi. "Bakuji nace karku zobane?"
Sunata kallonshi yanata kallon su, can budurwar ta nuna mishi kasan kofan wurinda glass ya fashe, iska na shiga. Yabi hannunta ya kalla kofan ya kalleta, fuskarshi ta nuna rashin fahimta. Tome take nufi? In bude musu kofa su shigo su badeni da CD? Ta kalla agogonta ta kalleshi.
"Inda munada CD, da tuni ka mutu."
Ashe tana magana. Me take nufida da tuni ya mutu? Oh! Hakanefa don ba a dadewa ake kamuwa a mutu. Tome zaiyi musu? Ko abincinda yake dashi bazai ishesuba, cin mutum dayane.
"Banida abinci."
"Ruwa mukeso, kuma yamma yayi muna bukatan wurin kwanciya."
"Toku tafi gidanku mana...."
"Inda munada inda zamuje zamuzo nan ne?" Gaskiya abin da hadari, Infa sun zone donsu cutar dashi? Yana cikin bacci su lahantashi. Kai, gwara kawai ya korasu.
Budurwar ta lura yana kokonton taimakonsu, suka hada ido da yarinyar sai yarinyar ta fara kukan kishi, tana jan rigan budurwan tana kuka. Budurwan ta kalleshi. "Don Allah ka taimakemu da ruwa, tun dazu take jin kishi amma bamu samu ruwaba."
Abu yayi dan jim sannan ya wuce samo ruwan. Bacewanshi daga wurin keda wuya yarinyar tayi shiru. Budurwan ta kalla yarinyan ta gefen ido sukayi murmushi. Ya dawo daukeda ruwa cikin robobi biyu ya mika musu ta inda glass ya fashe. Budurwar ta karba daya taba ma yarinyar daya. Kafa kai sukayi saida suka kwankwade duka.
Hamma yarinyar tayi ta kalla abu. Tabdi! Mema take nufi? Ai kawai su kara gaba. "To sai anjima, ku rike robobin." A mamakin shi sai ganin yayi sun kama wuri sunyi zamansu. Lallai wadannan suna ja dashi. "Wai meyasa bakujine? Na baku abinda kuke bukata ba saiku tafiba?"
"Dayan bukatan fa?"
"Wace bukata kuma?"
"Wurin kwanciya. Mun gaji, don Allah, ka taimaka, Please." Ta sassauta murya. Abu ya kalleta da kyau, da batayi turanciba da bazai taba cewa tasan A ba. Suma daga gani juyin rayuwane ta samesu saboda CD. Basu yi kamada junaba don budurwar chocolate ce, yarinyar kuma baka wuluk, ko don dattin da sukayine, kalansuma ta dishe.
"Da sharadi, in kuka so cutar dani zan fatattakeku daga gidana". Budurwar nata kallonshi can ta murmusa kadan.
"Ba damuwa."
Kwance yarinyar take kan gado tana bacci. Abu na zaune a palo yana goge video cameran sani yana tuno abokinshi. Toshi miyema matsayarshi in harya fita a raye daga annobannan? Zai rasa aikinshi, gidanshi, saidai ya koma jaki local government inda uwarshi take.
Juyowarshi keda wuya saida zuciyarshi tayi rawa. Budurwarce tsaye a bayanshi ta dasa mai idanu. Ya mike tsaye da sauri rikeda cameran yana kallon hannunta in babu makami. Ta nuna cameran.
"Takace?"
"Ina ruwanki kona wanene. Meya fito dake, karki ce min kuma wani abin kike nema?" Tana kallonshi tana tafiya harta zauna a kujera
"Na kasa bacci."
"Toya kikeso inyi dake? Inje in miki wakan bacci ko in miki nanayene?" Haba ta kwashe da dariya. "Ko daya, meyasa ka yarda ka taimaka muna, naga da kana kokonto?"
"Meye sunan?"
"Jidda, kaifa?"
"Abubakar, kirani abu."
Dalili dai dayane, tausayi. Sun bashi tausayi sanda yaga sun zube gefen gidan sunyi zamansu. Dukda akwai hadari tartare da taimakonsu, imaninsa baisa ya wulakantar dasuba.
"Meye labarinku?"
* * * *
SAFIYAN ANNOBA
Cikin gidan yawa dinnanne na haya, kowa nata harkarshi. Wani mutum ya shigo ya manna kanshi da bangon dakin su jidda. Jidda ta fito sagale da jakan hannu brown, sanye da riga da skirt light peach, gyale ja takalma flat peach tana sauri ta tuna ta manta wani abu, ta koma ta dauka ta fito tasa agogonta a wuyan hannu ta ciro wayarta tana kira tana kallon mutumin. Samarin biyu suka shigo suna sallama, 'ya'yan mai dayan dakin dake kusada nasu jiddane.
Wuce mutumin da suka yi keda wuya ya fadi kasa baya motsi. Jidda na cikin amsa sallama tayi tsit, idanunta suka fito a tsorace. Daya daga cikin samarin yaje ya taba mutumin yana girgizashi kozai tashi. Mikewan saurayin keda wuya ya zube kasa shima ba motsi. Dayan saurayin ya rugo a guje yana kiran ado ado ya zube a kasa yana girgiza ado. Shima ya zube kwance a kasa ba motsi.
Ihu jidda ta kwala ta sankare a inda take tsaye, mata ta fito daga dakin su jidda tana tambayan lafiya. Jidda na tsaye ta kasa komai sai zaro idanu tanata kallon kasa. Idanun matar sukabi inda jidda ke kallo tayi salati zataje wurinsu jidda ta rikota da karfin Allah.
Dattijo ya shigo hankali a tashe kawai sai yaga mutane kwance a kasa.
"Subhanallah ta iso har gida...". Ya balla a guje yabar gidan. Matar dake gefen jidda ta sulale ta fadi kasa bata motsi. Numfashin jidda yayi sama.
"Inna lillahi, Inna lillahi, anti, antina.....an...anti?" Muryata a shake. Sai ji tayi ihun jama'a ba dama a waje, kaman an tara mutane hamsin sun kwara ihu lokaci daya. Kirjinta ya harba sama gabadaya ta rikice. Taje a hankali ta leka waje, 'yan unguwansune da kila wasune sai zubewa a kasa sukeyi tun daga inda gidansu jidda yake zuwa saman layi. Kafin ta gama samun karfin gwiwan fitowa waje, gabadaya mutanen bamai motsi.
Nishi take tayi tana kallon mutanen hawaye na zuba daga idanunta. Wata budurwa ta ballo da gudu tana ihu tana cewa annoba ta kashe kowa. Tana isowa kusada jidda ta zube kasa bata motsi, jidda ta lura da kyau taga ta mutu, data sampe a guje baji ba gani.
Gudu take tana haduwa da mutane sunata faduwa suna mutuwa. Isowanta sand street keda wuya ta wuntsule ta fadi kasa tanata mulmula cikin kasa harta fada tabo. Ta dago daga tabon ta zauna, can ta fara kuka. Antinta da ita kadai ta rage mata a duniya ta rasu, yanzu batada kowa a duniya da zata kira dan uwa.
Ta taso marainiya, antince ke mata komai a rayuwarta, tun daga yarintarta har girmanta, karatunta ita ke daukan nauyinshi. Gashi a poly take karatu ta kusa gamawa amma yanzu data rasa gatanta wazai cigabada biya mata bukatun makaranta. Shike nan karshenta yazo.
Ta mike tsaye kafafunta na rawa ta fita daga tabon. Kayanta duk sun babbarke sun canza launi, gyalenma can ta tsinceshi ya zama tsumma. Ta kalla inda take batasan nan ba. Tayita tafiyan awowi ta huta nan ta cigabada tafiya harta shigo wani layi, ko'ina gawa ne kwance. Inama zata to? Duk inda ta wulga gawa take cin karoda kuma....ta taka burki.
Tsaye rikeda makamai wasu mutanene sun kai biyar sun jeru a bakin sound street. Suka mata gargadin karta karaso, kosu kasheta. Tofa abin yayi tsananine haka? Ta rufa ma kanta asiri tayi gaba. Tafiyanta keda wuya duka mutanen biyar suka zube kasa a mace.
Rana na kunan jidda amma tafiya take tayi, tun tana ganin mutane masu rai harta dena ganinsu saidai gawa kawai duk inda tabi, sunyi dambu. Tun tana fargaba harta saba. A cikin dan kankanin lokaci harta saba da ganin gawa kuma hankalinta ya rage tashi inta gansu.
Kukan yaro taji data yi wata kwananda ya kaita harmony road, tanata kallo taga inda rai yake donta dade saidai taga gawa. A cikin tulin gawawwaki ta hango wata yarinya karama zata kai shekara biyar, zaune kusada wasu gawa amma kuma yanzu ta bar kuka, bakinta kawai ke motsi tanata kallon gawan.
Daga gani kila iyayentane. Jidda ta karaso inda yarinyar take tanata kallonta kaman bata taba ganin mutumba. Yarinyar tanata motsi da baki tanata cewa mama. Jidda ta yunkura zata taba yarinyar saita tuna da yanda samarin nan suna taba mutum sai mutuwa. Can yarinyar ta kalla jidda idanunta sunyi ja.
"Mamana."
Jidda ta kalla matar dake kasa ta kalla yarinyar. "Bata, ya sunanki?"
"Falmata."
"Fally, sunanki kenan."
Saiji sukayi karan jiniya ta motar sojoji. Da sauri ta jawo hannun falmata suka ruga a guje suka bar unguwan. Sunsha tafiya kaman ba gobe kafin suga kwanon tuyan awara a gefen titi, awara na yawo cikin mai. Cikin hanzari jidda ta tsamoshi daga mai, yayi sanyi man, ta mikama falmata wasu taci wasu. Bayan sun gamaci suka diba hanya kuma.
Sunci karoda gawawwaki har sun gaji. Har wani mai rai yazo gabansu ya fadi a mace, suka kalleshi kawai sukayi gaba abinsu. Tafiyansu ta kaisu gidan gona mai suna Umar farm house. Isarsu keda wuya sukaga mutane a cikin gate din gidan. Mutanen suka sankare suna kallonsu jidda.
Wata mata tazo kusada gate ta tsaya tana kallonsu. "Meya kawoku nan?"
"Abinci", jidda ta amsa. Wani namji yazo. "Babu abincinda zai isa wasu mutane kuma ladidi, bazamu iyaba. Baiwar Allah, ku taf.....sai ganin yayi ladidi ta zube kasa". Idanunshi suka zaro ya kallo su jidda, suna kallonshi kaman ba mutuwa akayiba. Shima ya zube kasa a mace, sauran mutanen wurin suka fara gudu da iface iface.
Jidda da falmata nata kallon su har saida duka mutane kusan ashirin suka bar motsi. Jidda dai batasan meye cutar nan ba amma dai tasan cutar bata kasheta hakama yarinyarnan. Da kuran ta lafa, jidda ta bude gate suka shiga cikin gonan. Sukaga dabbobi iri iri, rago, tunkiya, akuya, zomo, kaji, hadda rafin kifi. Akwai gida a gefen gidan awakin, jidda ta bude suka shiga, palone karami, da daki a gefe sai kicin inda jidda ta nufa ta fara neman abu daya, abinci.
Zaune suke suna cin doya fara da sauce, a palo. Jidda ta kunna t.v. Anan ne taji bayani akan CD daga director din NDCC doctor john. Dukta fahimci bayaninshi, abinda bata ganeba shine, meyasa cutar bata kasheta amma kuma duk inda ta shiga sai an mutu? Kota makalene da jikinta yadda duk inda ta shiga sai kawai yabi iska...hakane fa, iska takebi kaman yanda doctor yace. Haba shiyasa duk inda sukaje sai an samu mass death dinnan. To kenan suyi zaman su nan tunda akwai abinci da ruwa da go...
"Suma sun mutu." Jidda tanata kallon falmata. To suwa suka mutu? Falmata ta nuna mata waje. Fitan jidda keda wuya sai taga duka dabbobin sun mutu. Tabdi! Ta zama annoba... A'a sun zama annoba dai, itada falmata. Dole Su bar wurin nan don na farko bazasu iya kwashe gawawwakinba kuma zasuyi wari in suka kwana. Taya za ayi su zauna cikin wari ai sai wata cutar ta kashesu. Amma....
Karan motoci sukaji, jidda takama hannun falmata suka boye gefen gidan. Sojoji biyar suka fito sanye da mask suna kallon filin gidan cikeda gawa. Daya yana magana ta wayan kunne, ya gama maganan yace da saura in sukaga mutane a raye su harbe....tuni jidda taja hannun falmata suka lallaba suka gudu. Ashe soja daya ya gansu yace a bisu da hannu. Yace ma sauran sojojin suyi shirin harbi da tranquilizer gun(bindigan sa bacci).
Sunyi gudu harna inna naha, da kyar suka guje ma sojojin da sukabi inda mota bataza iya shigaba. Suka bullo ta titi suna tafiya, kaifin idanun jidda suka hango shago rabinshi bude. Dama kishi ya ishesu kamanme saita nunama falmata shagon, suka ruga da gudu kwatsam sukaga mutum ya fita a guje kaman mahaukaci daga shagon. Suka taka birki gefen titi sunata kallon bayan saurayin yanata falfalawa da gudu.
Kallon juna sukayi suka kalla shagon suka karasa. Roban ruwane ya kai kwata a kasa yanata zubewa, falmata zata dauka jidda ta bige hannunta.
"Fally kar kisha ragowan wani, ga sabo". Taba falmata wani roban ruwa bayan ta bude mata itama ta dauka wani roban ruwan. Suka sha juices iri iri sukaci snacks kala kala cikinsu yadan taso don a gudunsu na dazu duk sun zazzage doyan da sukaci. Bayan sunyi nak sun huta jidda takama hannun falmata suka fita daga shagon da dan guzurinsu.
Isarsu mild crescent sai wasu almajirai su biyu suka sankare a tsaye suka rike wuya a tare, suka fadi kasa suka hau birgima, kura ta fara tashi. Jidda da falmata suka kalla juna suka maida kallo ga yaran. Menene kuma wannan? Badai wani sabon abu bane? Can kuran ta lafa sai sukaga almajiran sunbar mosti. Mamakin ya kamasu, jidda taja falmata suka bar wurin domin al'amarin cutar nan da mamaki yake. In wani sabon cutanne ai gwara suyi nisa da wurin basu saniba ko sabon cutar zai iya kashe su.
Karo suka dinga ci da kwararan mutane masu sabon cutar nan, jidda ta fara timing din tsawon lokacinda suke dauka kafin su mutu. Ta kadu da result din, minti biyar kawai. Dukda hakan shi sabon cutan nan ai yafi tsohon donshi tsohon mutuwa kawai akeyi ba sign. Amma sabon cutar tafi tsoro don kana ganin mutum na hakin mutuwa radadinta ya nuna a fuskanshi.
A rediyo a wani gida sukaji a news cewa ai itade ce cutar wancan ta farkon take ta kashe mutane, shiyasa gwamnati keta rokon jama'a dasu zauna a duk inda suke don rage yaduwar cutar. To ita cutar ta canza salone? Ikon Allah, akwai hadari yawon dasu jidda keyi amma ya ta iya?
In suka tsaya wuri daya, sojoji suke binsu zasu kashesu, in basu fita neman abinciba, abinci ze kare kuma dole su fita nema, in suka fita neman abinci, mutane da yawa na mutuwa ta dalilinsu, in suka tsaya cikin gida, su zasu mutu ta dalilin yunwa. To kunga, dolene su fita tunda abincin ba zuwa zaiyi ya samesuba.
Haka dole suka bar gidan donba abinci saidai ruwa. Sukayita haduwa da mutanen birgima, sunan da suka sama mutanen kenan. Sai sunyi birgima sun tada kura sannan su mutu. Idanuwansu sunga mutuwa da yawa a kankanin lokaci, mutuwa mai tada kowane irin hankali, zuciyoyinsu sunyi tauri ta dalilin rasa masoyanda sukayi, basuda kowa a duniya sai junansu.
Don cutar bata kashesu, suma sunsan ba daidai bane su yadata. Duk sanda suka haduda mutane birgima sai jidda tayi timing taga tsawon lokacinda suke dauka kafin su mutu, kara kaduwa take tayi domin abin yanzu ragewa kuma yakeyi, a mutum na sha daya sun samu minti hudu.
Masu kwasan gawa sunata kokarin kwashe inda gawan basuyi yawaba, su jidda dai sunata kokarin boyewa daga su hardai masu daukan samples daga gawawwakin.
Sun shiga wani kwana tsakanin gidaje sai sukaga kura ta tashi a gefen hanya inda gidaje suke. Jidda na labe itada falmata suna kallon kuran, lafawan kuran keda wuya sai sukaga mutumne ketayin birgima a kasa kaman kwari dubu sun lullubeshi sunata cizo. Can sai yabar motsi. Suka kalla juna suka maida kallon gareshi.
Tsura mata ido abu yayi, lallai taga ata, ace mutane tun kwanaki da suka wuce basuga hutuba sai tashin hankali, shiyasa suka kode suka lalace haka. Kashin wuyan jidda ya fito, idanunta sun fada, baisan ko sirintarta bane ko kara sirincewa tayi, Kayanta ba ako magana kaca kaca suke.
Jidda ta boye mishi wasu bangare na labarinsu. Ya za ayi ta gaya masa duk inda sukaje sai mutane sun mutu? Ko kuma har sojoji ke binsu? Ai saiya koresu karsu jawo mishi fitina. Wani abin mamakin da farin ciki shine, shima baya kamuwa da cutar a yanda ta lura. Shiyasa data ganshi tun lokacin nan a kofan palonshi ta gwadashi taga bai mutuba.
Bayan wahalan da sukaci, ta gaji kamarme so kawai take ta kwanta shiyasa ta dumfaro gidanshi. Aiko dole tayi farin ciki don bai mutuba. Komame ke hana cutar kashesu ta musu daidai, donda tuni sun sheka barzahu.