Iska ya kada ya kwashe kura yayi sama sararin samaniya sannan ya dawo kasa ya baje tareda bin gawawwakin dake kwance birjik a hanya. Kowane unguwa da nashi gayyan gawa. Yau kwanan gawawwakin goma kuma kullum sai an samu sababbi saboda rashin jin wasu mutane na a zauna a gida.
Garin rose gabaki daya wari yakeyi na fitan hankali, gawawwakin rubewa sukeyi da sauri. Sababbin gawan ma sunfi rubewa da wuri. In har haka yacigaba mutanen rose city zasu kare ai. Wasu kam suna gida a killace, wasu na isolation center, wasu na asibiti a killace, wadanda kawai ciwone ya kwantar dasu.
ROSE GENERAL HOSPITAL
Babban asibitin rose kenan, gidan sama mai hawa hudu yana daukeda dakuna 300. A kulle asibitin yake, wadanda ke ciki na ciki ba shiga ba fita. Iska ya kado labulen windon room 100, patient dake kwance tana taba waya kawai taji kaman an watsa mata kayoyi a wuya. Tayi watsida wayan ta rike wuya tana kaki, jini ya fara fita daga hancinta da baki kalan jinin ya kusa zama baki.
Wayan patient din ya gangara ya buga kofan bayi. Kofan ta bude, budurwa ta fito, fuskarta a jike ta gama alwala taci karoda waya ta duka ta dauka ta kallo budurwar kan gadon. Da sauri ta isa inda take ta zaro idanu da taga jini na fita daga hancinta da baki, bakin jini!
Da gudu ta fita daga dakin tana kwalama doctor kira amma duk inda ta wulga shiru. Asibitin ya cikada mutane dazu, yanzu duk ina suke? Karya kwana keda wuya taga wani tsohon rikeda wuya, jini na fita daga hancinshi da baki. Hankalinta ya tashi taja baya ta canza hanya, duk inda tabi, mutanene ke mutuwa ba adadi, harda doctors da nurses, ga yara da manya kai kowa faduwa yakeyi suna jini suna mutuwa. Kanta ta rike a kidime ta rafka ihu ta sume.
ROSE RESEARCH CENTRE
"Doctor Mrs noor, ya any progress?" Doctor noor ta dago kai daga papers a office dinta ta kalla mai magana. "Not yet, kubra. I need to take some more tests". Noor ta mike ta wuce kubra ta fita daga office dinta. Kubra tabi bayanta har suka iso kofar lab. "Did the director ask you to tail me and slow me down on my job or is it a habit for you?"
"Hahhh haba de.....". Noor ta tsura mata ido. "Shine, to ya zanyi? Duk sanda ya ganni saiya tambayeni any progress. Nasan shima an azalzaleshine, shine nima yazo ya addabeni".
"Shine nima zaki dameni? You of all people should know, there's no rush a irin binciken nan dole mubi abu dalla dalla. We need accuracy not speed alone. You back off! and tell him to back off!!". Ta bangaza kofan lab ya bude ta shige tabar kubra tsaye tana kallon kofan. Canta wuce abinta tareda wurga hannayenta.
Kwararriyar likitar binkice noor asad, ta kware a nemo maganin cututtuka da dama, irin cututtukan da maganin su keda wahalan samu, ko cututtukan da ba a taba majinsuba. Tana identifying cuta, ta gano gubanda cutan tasa a jikin mutum kuma ta gano maganin guban cutar.
Tun farkon faruwan annoban nan an hana fita koda ko medical personnel ne, saboda tsananin hadarin cutan. Inba likita nada aiki muhimmiba, baza a bari ya fitaba kuma in zai fita sai tareda sojoji.
Noor ta shiga isolated CD test lab, sanyeda hazmat suit. Daukeda samples din jini kala kala cikin EDTA bottles (roban ajiyan jini kafin ayi test). Ta ajiye ta fara tests, ta diga wannan reagent ta diga wancan reagent tayi viewing a microscope. Taja baya da sauri, ta kara manna Idanunta wurin kallo a microscope din, what!!!
Zaune a lungu noor ta labe tana waya da doctor mary ta NDCC. Dama turota akayi daga can tazo tayi binciken samples din da aketa kawowa lab kuma tayi reporting directly to NDCC. Rikidan jinin wato mutation yayi tsanani yanzu, donda shigan CD jinin mutum, yake canzawa gabadaya ya kashe mutum nan da nan. Yana kai harine ga jijiyoyin jinin dake wuya da hancin mutum, ya fasasu gabadaya. Duka berayen da tayi testing sun mutu suna fidda jini ta hancin da baki.
To kenan in waves cutar take gudana? Mary ta tambaya. Hakane, wave na farko shine (jagular strangulation) shakewan wuya. Na biyu, (convulsion) girgizan jiki ba a cikin hanyaciba. Na uku, (bleeding from the nose and throat) fitan jini daga hanci da wuya.
Gawawwakin berayen da tayi amfanida sun rube na fitan hankali bayan awa biyu kawai da mutuwa. Abin daya tada hankalin noor shine it takes 5 seconds for rats masu rai su kamuda CD da aka hadasu da berayen da suka mutu dagashi. What!! Speed of contact is five seconds!!! Mary ta tambaye noor adadin lokutan da cutar keyi a iska kafinta mutu. A gwaje gwajenta ta gano awa biyu CD keyi a iska kafinta mutu. To maganan maganin fa?
Don daman noor ta bukaci samples na jini daga mutane daban daban koda za ayi dace a samu mai rigakafi a ciki. Duk jinin da aketa kawowa tests take tayi. Kuma ba ayi dace da samun rigakafin ba a jinin. Tana bukatan karin samples.
Haduwa noor tayida doctor George a office dinta ta bukaci karin samples, amma ba irin wanda suke kawo mataba. Jinin asymptomatic take bukata, wato mutanen da basu nuna alaman CD tare dasu, to jininsu take bukata.
Abinda wahala, tayaya za ayi yasan wake daukeda cutan kuma bai nuna alamaba? George ya tambaya. Subi mutanenda suke gani suna yawo tsakanin gawawwaki su samo jininsu. Don wanda baida rigakafin bazai dadeba a wurin gawan zai kamuda CD ya mutu. Kuma suyi sauri don tana bukatar abin da gaggawa.
Idanunta na marmar ta budesu ta sankare, wasu idanun ke kallonta.
"Sannu baiwar Allah kin farka. Sumewa kikayi na ganki na goyoki na kawoki nan. Naga lokacin da kika sume ai, shiyasa cikin zafin nama na daukoki na kawoki nan. Saida na duba naga kinada pulse, sannan na daukoki ba kaman sauran ba." Mikewa zaune tayi tana kallon inda take can taji wani suka mai kaifi ta goshinta ta taba taji bandeji.
"Ai buga goshinki kikayi da kika fadi, dayake ni chew ce shine na miki dressing. Ya kikeji yanzu?"
"Laf...ina take?" Ta tuna wani abu.
"Wace?" Chew din ta tambaya.
"Maryam, ina maryam take?"
"Jini ya fita a hancinta da baki?" Ta kada kai. "Tab! Wannan aita tafi, mutus ta mutu, in kiyasce miki duka asibitin nan kowa ya mutu mu kadai muka rage".
"Inna.....Inna...wayyo kina son kice min.....maryam ta mutu?!"
"Ke danace miki kowa ya mutu, 'ya ta da mijina duk sun mutu, daga mun kawo zulai ba lafiya shikenan akace annoba ta bullo kowa ya tsaya inda yake. To gashi annoban tazo har nan ta kashe minsu". Kallonta budurwan ke tayi. "Wacece ke?"
"Aw sai yanzu hankalinki ya dawo? Sunana tani, kefa?"
"Shukura, na shiga uku maryam ta rasu".
"Ke daya fa kika rasa nifa dana rasa biyu sai in fadi kasa kenan in mutu". Shukura ta kalla tani, lallai matar nan batada sense of sympathy, ina ruwanta in duniya guda ta rasa, ita dai kawai wadda ta dameta sani. Hawaye suka gangara kan kumatunta ta mike tsaye zata fita.
"Kuma ina zuwa? Baki san annoba ya cika asibitin nanba kikeso ki fita kema tayi aw on gaba dake. A iska akace cutar na yawo shiyasa na rufe dakin nan rufff."
"Ke keda rayuwata? Toko tunda bake keda itada dole kibarni inyi yanda naga dama da ita."
"To Allah huci zuciyanki, ina ruwan kumurci sarkin fushi, nidai a kullen kofa in an fita."
Shukura ta bude kofa ta fice ta barshi bude. Ta koma dakin 'yar uwarta shigarta keda wuya wani wari ya bade hancinta taga gawan maryam a langwabe, busasshen bakin jini makale da hancinta da bakinta, kalan jikinta ya canza yayi bororo yana fitarda ruwa mai wari. Hawaye suka gangaro kan kumatunta tayi sauri ta fita.
Ai gabaki daya ta firgita data fita taci karoda tani. Meya kawo matarnan nan kuma? Tani ta kada baki. "A gabana mutane da yawa sun mutu anan asibitin, amma koda wane daliline, mu kam bamu kamu dashiba". Shukura ta wuceta ta biyota. Suka fita daga asibitin gawawwakine birjik ko'ina. Shukura ta rike kai a rikice, hawaye sai gangarowa sukeyi daga idonta, ga wari na tashi na gawawwakin.
"Tab! Wannan hawaye kaman tekun maliya ke kam ai saiki gama da hawayenki indai don hakan ne".
"Wai meyasa bakida tausayine! bakida imanine!! Ko hauka ke damunki!!! Mutanene suka mutu ba dabbobiba!!!" Da ihu shukura ke kuka tana magana, ta cigabada kuka, tani tayi jim tanata kallonta. Tsautsayine ya kawota garin nan.
* * * *
Bus luxurious ya cikada pasinjoji, conductor ya karba ticket din kowannensu ya bula da puncher ya basu yaje seat din gefen driver ya zauna. Mota ta tashi daga long station, golden city zataje rose city. Mutanen ciki wasu nata annashuwa, wasu na addu'o'i, wasu na hira, wasu sunyi shiru suna kallon titi.
Shukura ta kura ma titi idanu tana tuna 'yar uwarta maryam da akama fyade. Kanta ya buga da taji labarin daga mijin mamanta. Dayake mamanta bata tareda babanta, shukura kuma na zaune tareda maman. Maryam na wurin baban.
Yama akayi wai har gadafi yayima 'yar kanin babanshi, maryam fyade? Kuma the most annoying thing ma shine, ba a mishi komai ba. Ba fada ba zagi, haka aka sa mishi ido yana tafiya free yana takaman yayi din. Ko donsu sunada kudine? Aikin banza.
Dama shukura bata shirida gadafi saboda shaye shayenshi, tabace, wiwi, sholi, ba abinda bai sha. In yayi nak yayita zuba rashin mutuncinshi. Toma wai ya akayi hakan ta faru? Ita dai maryam ga kiba kuma kakkarface, har ya akayi yayi overpowering dinta?! Canta tuna yanda 'yan gidan ruma kaman giant suke, ga girman jiki ga karfi.
Wane irin rashin adalcine haka? Ko don uwarta bata gidanne? Sai kishiyoyin uwar kawai. Wai ace har babanta ya kasa yin wani abu akai? Bayan mijin maman shukura ya gaya mata abinda ya samu 'yar uwarta saita buga mata taji yanda akayi hakan ta faru.
Kuka maryam ta bade kunnen shukura tana gaya mata gadafi yaci mutuncinta ya kauda budurcinta ta shiga uku ya zatayi? Maryam ta tabbatar mata da cewa duk family an sani ta fallasashi amma ba wanda yayi wani abu harda uban nata shima shiru kakeji kaman ruwa yaci gari. Ba shiri shukura tace gata nan zuwa the next day. Tayi booking ticket yanzu gata a bus.
Tunaninta kawai yanda zata watsashi a police station, daga nan a watsashi a kotu, daga can su watsashi a jail tambadadde kawai. Wallahi bataga dai riban haihuwarshiba, sai jawo musu rigima yakeyi a family kuma an rasa mai kwabanshi don a gidan uncle ruma shi kadai ne namiji duk sauran 15 din matane. Wannan da haihuwarshi dama cikin zubewa yayi a lokacin. Tun yanayi a waje yanzu abin ya dawo 'yan gidama basu tsiraba?
Mtsssw barinshi akeyi shiyasa yake cigabada iskancinshi. By the time she's done with him, zai ganeda cewa ya tabo garwashine. 'Yar uwarta tilo da su biyune kawai wurin iyayensu shine zai kamata yayi mata haka, wallahi saiya gane kurenshi.
Sha kuruminki maryam, an cuceki, anci mutuncinki, ni 'yar uwarki, zan miki yaki. Shukura tacema mamanta basai taje rose city ba inta gama cin kaniyansu zata dawo musu da maryam, har mijin maman ya amince don baida matsala suna zaune lafiya dashi.
Sako shukura ta turama maryam cewa ta iso tana gidane? Maryam tace tana gidan kawarta yanzu saboda zuwan shukura taje can donsu hada plan din yakan mara mutuncin can. Ta tura mata da address, shukura ta dauka mai napep ya kaita can.
Shukura ta bukaci tasan abinda ya faru harya kaiga haka. Ashe dama ya saba inyaga maryam saiya nema abin tabawa a jikinta. Ranar kuwa ta dalla mai mari daya shigo dakinta ya baje gefenta tana kwance ya hau tabata. Marin shi keda wuya ya hayeta ya danne ya toshe bakinta yaci mata mutuncinta son ransa. Harda ce mata ta gayama duk wanda zata gayama ba abinda aka isa a mishi.
Police station na harmony street zasu kai kara a cafkoshi saisu shigarda kara a kotu duk a yau din. Mijin maman shukura yayi mata transfer kudi enough da zata yi duk abinda ya dace.
"Yanzu yana nanne koya koma dazzle?", shukura ta tambaya.
"Yana nan tukun ance ogansu na wurin aikinshi a dazzle ya sashi wani aiki anan garin." Maryam ta kara bayani. Haka suka gama komai a ranan. Akaje aka kamoshi aka kai police station. Sai su uku shukura, maryam da hawwi sukayi shiru suji mai munafukan 'yan uwansu shukura zasuce yanzu da aka kama dan gaban goshin su.
Habawa! Faruwar haka keda wuya ko awa daya cur bata cikaba shukura tasha kira harta gaji dontace a bada lambarta ga duk mai neman belinshi ya kirata tukunna kafinta amince ayi belin gadafi, hm kaman zata amincene. Tasha ashar wurin mata, zagi wurin maza da mata, cin mutunci, har uwarta aka kira ana zagi, amma sun manta cewa 'yarta aka cuta, kuma dansune ya aikata hakan.
A saboda haka taki beli. Washe gari, shukura takai maryam asibitin rose saboda tanada ciwo a gabanta don saida ma aka mata dinki. Hasabibin, ya dagargaza mata jiki, la'ananne kawai. Isarsu asibitin saiji tayi kawai hawwi ta bugo tana gaya mata an sakoshi. Daga nan kuma sai barkewar annoba kashi kashi.
* * * *
Oh, yanzu ta rasa 'yar uwarta sweet maryam dinta. Koya shi kuma wancan la'ananne? Halama ya mutu don kowa mutuwa yake tayi. Don inbai mutuba karma yayi fatan haduwarshi a ita wallahi, yanda zatayi rugu rugu dashi ko CD sai haka.
Komawa tayi dakinda gawan maryam take, tayi mamakin ganin yanda gawan ta kara rubewa tana dagargajewa tana fitarda wani azababben wari. Ta toshe hancinta tayi mata addu'a ta dauka bed cover ta rufeta ta dauka wayarta da jakarta dana maryam ta fito hawaye na bin kumatunta. Ikon Allah kaman ba dazunnanba suke magana da maryam daga shiga tayi alwala har maryam ta rasu. Ta dawo dakinda tani ta kaita tayi sallah ta cigabada kuka. Ta kira lambar mamanta.
Hafiz ya kalla Asiya suna tsaye a glass balcony na boss office, ta kalleshi tayi murmushi. Wannan smile din, ya ishe shi farin ciki for today. Ya lura hankalinta ya tafi wani wurin. Me take tunanine? Shi kanshi tunanin abbas ya isheshi, koya isa dazzle ko bai samu ya fita rose ba. Aida ya kira shi indai ya fita daga rose. Kodai ya kirane? Nooo bari dai kawai ya bari a kira shi tukunna, wannan tension yawa gareshi amma yau 5 days kenan da tafiyar abbas. Messages basu shiga phone dinshi, har yau? Allah sa dai lafiya.
* * * *
KWANA BIYAR DA SUKA WUCE
7:15pm
T.v naci a reception, hamid na zaune shida farouk suna kallon news. Ummi ta sauko daga stairs ta iske hamid. Kash! Wannan bazai bar kallonta bane? Tunda ta fara saukowa daga stairs yaketa kallonta, Allah yasota ma bataci tuntubeba ta watse a kasa, aiko da tasha kunya, wai!
Wani ya wuce farouk, ya dasa mata idanu malam ko kiftawa bayayi. Ta hade gira tayi sauri ta wuce wurin yayanta. Hmm malamin harda karkatowa yayi yana jin dadin kallon. Ummi ta zauna gefen hamid ta hararo farouk, yayi murmushi ya cigabada kallonta.
Asiya ta sauko sagaleda backpack a bayanta, rikeda leda cikeda guzuri, dayan hannunta rikeda keys din pharmacy, bayanta usmanne rikeda wata leda. Tazo kusada ummi ta tsaya.
"Ina naku?" Asiya ta tambaya.
"Yana wurin brother bukar." Hafiz da abbas suka fito daga office din Asiya daukeda backpack guda biyu, rike a hannaye abbas, yazo ya diresu a kasa. Kowa yayi shirin tafiya. Hafiz yana tunatar da abbas cewa muddin suka isa dazzle ya kirashi. Abbas ya sagala jakanshi mai daukeda guzuri ya kalla usman ya tambayeshi inya shirya usman yace eh.
Asiya tana satan kallon yanda arms din hafiz su kayi kato rigarda yasa ta matse muscles dinshi yayi kyau. Ummi ta zungureta ta daga mata gira irin yadai, yayine? Asiya ta murmusa. hafiz da farouk suka sagala backpack dinsu.
Yanzu ga yadda tafiyan zata kasance. Dama abbas zai tafi dazzle tareda usman, ummi zatabi hamid da bukar su koma gida, farouk zai tafida Asiya gida amma kuma saime? Hafiz yace lallaine bazai barsu su tafi su kadaiba saiya raka Asiya har gida.
Abin ya ma Asiya dadi har a ranta. Abin yaba farouk mamaki da haushi, ya za ayi gashi nan kuma hafiz yace wai zai raka asiya kaman shi farouk din is not capable. Sam bazai yiwuba farouk ya nanata, tunda hafiz yazo rose city donya cece yarshi, to kuma lafiyanta lau basaiya komaba? Hafiz bai damuda rashin amincewar farouk ba domin shi da wata manufa ya dauka rakiyan wanda ya lura farouk ya dauka rakiyan da tashi manufar da daban.
Daga karshe dai kowa ya fita daga pharmacy ta kofan baya, Asiya tazo zata rufe, hafiz yace ta barshi zai tayata. Ummi tayi murmushi tana jin dadin yanda hafiz kejida Asiya. Kuskurene yasata ta kallo gefe ashe farouk ne a wajen.
Ya daga mata gira ta hade fuska ta juya. Bayan kulle kofa sukayi sallama da bankwana da juna, kowa yayi hanyanshi. Su hafiz sukabi kudu, su ummi sukabi arewa, su abbas sukabi gabas. Rashin hanyan mota da tsaro yasa dole suka bar motar Asiya. Ta die hard street dake makale da bold street sukabi.
Farouk yayima Asiya gargadi gameda abinda zata gani mai tayarda hankali. Sata sukayi a tsakiya suna tafiya suna labe labe in sunga sojoji. Sunyi tafiyana 20 minutes daga gawa sai sojojin suke cin karoda. Asiya ta kalla hafiz da farouk tana tunanin yanda wadannan mutane biyu suke kareta daga duk abinda zai cutar da ita.
Itace lucky girl ai samun masu kula dakai tsakani da Allah wadanda zaka iya dogaroda. Sannan kuma......harbi ya wuce ta gefen kunneta. Ba shiru taganta kasa warwas. Abin kaman a slow motion, kunnuwanta sun toshe sai ganin tayi farouk yana ihu amma bata jinshi kaman yana ce mata ta kawo hannunta.
Ta juya taga hafiz gefenta kwance a kasa dukda darene amma akwai wutan lantarki a gidaje dake haskawa, Idanunshi taga sunyi duhu kaman na predator sunyi focus yana kallon bayansu. Bin idanunshi tayi taga sojoji daga nesa suna saitosu da bindiga. Habawa karan harbi ta karaji tareda ihun farouk, cikin firgice suka tashi tsaye itada hafiz suka balla a guje sukayi wata kwana.
Wani gida suka shige suka labe. Farouk fa? Ta kallo hafiz idanunta a zare yayi mata alama da tayi shiru. Karan takun sojojine sukaji zuciyar Asiya ta bada damm. Hafiz ya leka ta windo yaga sunata nemansu, sai ganin yayi sun fara shiga gidaje, yasan in suka tsaya wurin sojojin zasu cimmusu. Duk inda farouk yake zai nemoshi wani lokacin amma yanzu dole ya kare asiya daga sojojin nan.
Why will they start shooting people? Waya basu wannan odan? Ai hakan bai daceba, lallai yanada mutanen da zai ci kaniya don sun kusa lahanta mai budurwa. Da baiyi zafin namaba ya turata kasa da...no way wallahi, saiya tabbatar iskanda suke shaka ya zamo illah a garesu, sai ya azabtar dasu.
Da sauri yayi ma Asiya nunin ta bishi, suka bar gidan suna labe labe. Bayan sunyi nisa da sojojin Asiya ta ciro wayanta hannunta na rawa ta kira lambar farouk, wayan na ringing amma bai dauka ba. Tayi kira ba adadi amma shiru, ta fara kuka.
"Baby please don't cry, am sure he's fine. Karki damu zan nemoshi but...". Sukaji karan motoci sun tsaya, wani soja yana bada odan cewa idan sukaga mutane su harba musu tranquilizer ga wasu masu gwaji zasu dauka jininsu. Labe suke cikin wani kango suna leken sojojin. Asiya ta sulale ta zauna hafiz idanunshi kan sojojin can yaga suna watsuwa nemansu.
Nan ma sukayita rabewa har sukaga kansu a depot din sojoji sunata gyaran tranquilizer guns suna tafiya operation. Hafiz yayima Asiya nuni da hannu tayi shiru ta biyoshi suka bar wurin. Ya duba agogonshi yaga karfe tara bai kamata suyita sintiriba a hanya tunda tsaron yayi tsauri a streets dinnan
Asiya ta girgiza kai tace a hankali su koma Ahmed pharmacy kawai. Don sunata zageyene an riga an rufe hanyan fita daga unguwannin dake zagayeda bold street. Sunbita die hard an toshe, sunbita bloom street an toshe, su dawo toshiba road nanma no way. Yanda sojojin ke aikinsu a ganinta ko kwaro bazai fitaba ai, halama farouk ya koma can pharmacy din.
Daga karshe dole hafiz ya yarda suka dawo ta die hard suka koma pharmacy. Kuma a hanyarsu ta komawa ba wata matsala har suka shigata kofan baya. Har Alla Alla take su isa pharmacy ko zata hango farouk amma ina bashi babu alamashi.
Asiya ta zauna a stairs ta hada kai da gwiwa. Abin duniya ya isheta, shiyasa bata son fita, tunda annoban bai lafaba, to ko tsaro bazai lafaba shima. Gashi yanzu sun sake rabuwa da farouk. Ko ina yake? Ya yake? Gashi taji harbi taji yayi ihu. Hawaye suka sauka kan gwiwanta.
"Babe please stop crying, bani number dinshi".
"Bai picking".
"I know I'll keep trying". Asiya ta bashi lambar farouk.
Kaman almara farouk kawai ji yayi karan harbi yabi tsakaninshi da Asiya. Waigawanshi keda wuya don yaga ta ina akayi harbin sai hango sojoji yayi, ji yayi kanshi yayi luuuu, can ya tunada Asiya. Ina take? Sai kawai ganinta yayi a kasa tareda hafiz.
"Asiya tashi! miko hannun ki muje!!". Harbi kawai ya sakeji ya tsala ihu da wani abu mai zafi ya bugo kafanshi. Kafa me naci ban bakiba ya arta a guje, har saida ya fara jin jikinshi ya fara nauyi. Karfi ya fara ragewa, wani mugun mutuwa jiki ya fara ji da kyar yake tafiya yana jan kafa. Idanunshi suka kai kan kafarshi yaga wani abu makale da ita.
Idanunshi suka fara nauyi yana ganin bibbiyu. Ya jingina da wani kofa a wani lungu, ya sulale ya zube kasa idanunshi suna rurrufewa, yana hango hasken bulb yanajin karan motoci kaman daga nesa sai dippp duhu.
Masifa kaman za a cinye ummi, don me zaisa tabi yayyinta bayan ance mata karta fita? Bayan tana ganin abin dake faruwa a gari, bata tsoron wani abu ya sametane? Meyasa ma bata bugoba? Kuma meyasa su bukar basu bugo sunce tana tareda suba? Sun san hankalin iyayen zai tashi amma ko a jikinsu. Hakuri sukayita badawa da cewa ai sun kira baije bane a musu afuwa.
Bayan kuran ta lafa, ummi ta watsa ruwa a jikinta ta dauro alwala tayi sallah taci abinci sannan ta dauka wayanta taga charge saura 1% tayi sauri ta makalata charging.
Wurin 8:35 pm suka shigo gida da yake basu haduda wata hayaniyaba sosai a hanya. Idanuwanta taji suna mata nauyi ta kwantar da kanta jikin gado sai illa masha Allah.
Bude idonta keda wuya sai akan agogonta dake nuna karfe 7 na safe. Ta gama abinda zatayi tayi sallah tayi wanka ta fito taga hamid yanata tura kofan gidan yaki buduwa tunda ta ciki ake turawa waje. Shida bukar sukasa karfinsu na bara suka tura saiya bude.
"Kaiii! Mutum!" Bukar ya sankare kanshi na leken waje, hamid ya tura kanshi waje ya fita ya leka fuskan da kyau.
"Tsaya wannan kaman nasanshi".
"Kaman wannan meyama sunanshi....umar", bukar yace.
"Sunanshi farouk", hamid yace.
"To ai duk dayane", bukar ya musa.
"Farouk dai ake kiranshi", hamid yaki amincewa.
"Farouk?!" Ummi tayi sauri ta fita tana kallon mutum kwance a kasa. Fuskarshi kaman yana bacci mai dadi, ta kura mai ido taga kirjinshi na tashi da sauka amma a hankali. Yana raye, amma maiya kawoshi nan? Ta maida idanunta ga kyakkyawar fuskarshi da dan sajenshi siriri daidai da fuskan.
Idonta suka gangara zuwa kafanshi taga wani abu a makale. Ta dan duka don taga ko menene, da sauri ta cizge abin daga kafarshi tana kallon abin. To miye wannan kaman allura guntu? Wait! To in yana nan, ina Asiya? Meye faru a hanyan su ta komawa gida? Allah sa dai lafiya.
Nan da nan hankalinta ya tashi tasasu hamid suka daukoshi suka kai dakin bukar suka jibge kan gado. Dayake tanada first aid box a dakinta da sauri ta ruga ta dauko, tasa scissors ta yage wandonshi har zuwa kauri taga inda alluranta caka yayi baki, wasu jijiyoyisun zagaye da wurin.
Tayi mai dressing tayi checking bp daidai yake 100 by 70, temperature ya dan hau 390c da pulse 80. Ta kai bayan hannunta kan goshinshi taji babu zafi. Saidai fuskarshi da jikinshi sunyi butu butu. Samo farin tsumman da takeji da bamai taba mata shi tayi da ruwan dumi ta fara goge mai fuska.
Hmm gayen nan fa ya hadu, ji giranshi mai kauri, giran idanunshi sun cicciko, ta goge hancinshi mai tsawo, tazo bakinshi ta taka birki. Lebbanshi so cute shiyasa inya mata murmushi sai taji damm a zuciyarta, lebban kaman an zana brown eye pencil zagaye dasu, ta ciki sama yayi dark brown kasa yayi pink.
Farin tsumman yabita gefen bakin farouk ya gangara zuwa dogon wuyanshi. Idanun ummi suka tsaya kan makwallatonshi, kawai taga yayi sama da kasa, zata janye tsumman daga wuyanshi taji an cafko hannunta da karfi. Kirjinta ya buga, tayi saurin daga ido ta kalla idanun farouk.
Kyarrr idanunshi akan nata, sun danyi ja amma bakin ciki na zagayeda brown. Yayi murmushi ya lumshe ido wanda hakan ya fizgota daga tunaninta taja hannunta yaki saki.
"Ka sakeni!". Yaki yanata kallonta murmushi manne a lebbanshi. "Ka sakeni ko in kwala ihu!!" Saime? Jawota yayi ya hada lebenshi da nata. Inna lillahi! Meke faruwane haka? Da sauri taja baya ta tsura mai ido cikin takaici. Ta kwasheshi da mari ne? kota naushi fuskarshi? kota...?
"Allah sa kada in tashi daga mafarkin nan, sooo sweet". Idanunshi a rufe yaketa magana.
Ai bakin ummi kasa rufewa yayi don tsabar mamaki. Wato waishi a zatonshi mafarki yakeyi?! Bala'i, yashata a banza kenan? Ta mike tsaye cikin fushi tabar dakin. Shigarta dakinta ta cizgo wayarta daga charging ta kira Asiya.
Asiya na ganin wayarta tayi kara da gudu ta dauka. "Farouk?".
"A'a, ummice, amma farouk yana nan, gidanmu".
"What!!! How?!" Hafiz na zaune gefenta a kicin yayi sauri maida hankalinshi kanta. Ta kalleshi ta maida wayan loudspeaker.
"Brothers nane suka ganshi a jikin kofan gidanmu a sume".
"What!!!". Asiya ta kidime.
"How's he now?" Hafiz ya tambaya.
"Hafiz?"
"Yes".
"Still yana bacci, but what happened? Ya akayi.....? Ina kuke?"
"Ahmed pharmacy", Asiya ta amsa.
"What!!! Kun koma kuma?! Why?"
"Saboda every street that leads out of bold, was blocked. No way in, no way out. shiyasa muka dawo". Hafiz yayi bayani.
"Asiya please ki hakura kizo gidanmu tunda ga kaninki nan". Asiya ta kalla hafiz.
"Zan kawota".
"Sai munzo". Ta katse wayan.