Chereads / TA ISO / Chapter 20 - BABI NA SHA TAKWAS SANIN JUNA 1

Chapter 20 - BABI NA SHA TAKWAS SANIN JUNA 1

Rana ta fara zafi dukda it's only 10am na safe. Hafiz da Asiya suna tafiya zuwa gidansu ummi saita taka burki hafiz yaga tayi. Jawabin data mishi yasa yayi mata kallon mamaki.
"Don't look at me like that".
"Why not? Ai inasha kawarkice? How comes ma baki san gidansuba?"
Asiya ta mai bayani of recent ne suka zama kawaye amma sun dade suna aiki tare. Turawa ummi tayi message tayi tana bukatan address din gidansu. Nan da nan ko ummi ta turo. Hafiz ya lura Asiya na goge zufan goshinta, yasa hannu a pocket ya ciro hanky ya mika mata. Tayi murmushi ta karba ta goge zufan.
Baddo road ne kadai hanya mafi sauki dazai kaisu amazon, unguwarsu ummi. Takawa sukeyi in sunji karan motoci su labe har sai sun tafi su cigabada tafiya. A bodan baddo gawawwakine birjik, can sukaga masu kwashe gawa nata fama. Wurga gawa na karshe sukayi a boot na pickup ya cika, suka shiga motan suka tafi zuwa birnewa.
Taku daya da hafiz zaiyi sai tear gas yagani an wurgo kusada kafinshi dayan kuma ta bayanshi inda Asiya take. Tuni wuri ya turnike da hayaki mai yaji. Asiya ta rike wuya tana tari canta sume, hafiz na ganin zata sume yayi sauri ya cafkota da kakkarfan hannayenshi ya sampe da ita a guje sai....pharmacy.
Sojoji na isowa sukaga wayam. Sergeant ya tambaya ina suke. Sojan da ya harba tear gas din ya tabbatar mishi da cewa nan ya gansu last. To bacewa sukayi without a trace? Sunan wani series. Sergeant ya bugi kan sojan ya juya ya wuce.
Duk inda hankalin hafiz yayi ya kasa kwanciya, shiba doctor ba, ba health personnel ba balle ya agaza ma masoyiyarshi. Gashi a sume take har bayan awa daya. Kwance take a kasa a reception, hafiz na gefenta cike da damuwa. Ya tsurama fuskanta ido yanda giran idonta sukayi zara zara dogaye a rufe, ya kalla sauka da tashin kirjinta a hankali, yanda yake tun sanda ya kawota.
Gaskiya aka kara awa daya bata tashi ba, dole yayi wani abu. Ya bata first aid na ventilation, wato ta samu iska sosai cikin huhunta don kore gas din. Wani tunani ya bijiro cikin kanshi, kai nooo infa ta farka tagansu a yanayin? Ai saita daukeshi dan iska, amma shi a yanzu rayuwarta yafi mishi komai. Gaskiya saidai taji haushinshi amma tension ya isheshi.
Hafiz ya tsugunna daidai kanta ya matse hancinta da yatsunshi, ya bude bakinta da dayan hannun ya gurfano kusada bakinta ya taka birki yana kallon wannan lebbanda suke bashi sha'awa har baya gajiya da kallon su. To infa yanzu ya kasa tsayawa? Yayi sauri ya girgije tunanin hakan daga kanshi, wannan shaidane kawai kemai zirya a kwalkwaluwa. Ceton rayuwarta yakeyi nothing more.
Lebbanshi na sauka kan nata yasan ya shiga uku amma hakanan da dauriya da imani da dagewa ya cigabada abinda yakeyi. Tome kuke tunani? Mouth to mouth respiration ne. Ya hura mata iska a baki ya shaka ya hura. Yayi hakan a sawu na uku ta fara tari.
Murnan daya bayyana a fuskanshi ba ako magana. Kaman ya rugumeta yakeji amma dole tasa ya danja baya. Bude idon asiya sai kan hafiz, ya share kwalla daga idonshi. Mamaki ya kamata, kuka yakeyi? To Meye zai faru yasashi kuka? Ko abbas ne wani abu ya sameshi.
Zumbur ta mike zaune Idanunta sun fito. "Abbas ne? Wani abu ya sameshine?" Hafiz yayi sekeke yana kallonta. Abbas kuma? Meyasa take tunanin Ab.....? "Naga hawaye a idonka. Please ka gaya min abbas lafiyanshi lau deko?" Oh! Shiyasa take sha wani abu ya faruda abbas shine yake zubarda kwalla? Allah sarki bata san itace silan zubar hawayen hafiz ba.
Lallai bata san irin sonda yake mataba. kuma baiga laifintaba don basu wani san junaba. Abubuwa da yawa sun faru da suka kasa barinsu su tattauna akan zancen zuciyarsu. Amma duk wannan zai canza, dole tasan ya yakeji gameda ita a zuciyanshi kuma dole ya nuna hakan a zahiri. Itama ya kamata yasan miye matsayinshi a zuciyarta.
"Abbas is.....I don't know, bai kiraba". Tunani ya bade kanta, to in ba abbas ba, me zai sashi hawaye haka? "It's you baby, hankalina ya tashi da baki tashi ba har tsawon awa biyu".
"Har na kai awa biyu ana....? Pharmacy?! Mun sake dawowa?"
Hakane, ya ya iya? It is the only safe place musu a yanzu. Wayarta yayi kara ta kalla backpack dinta gefenta ta jawo ta bude ta ciro wayarta taga ummice, tasa wayar a loud speaker. Ummi ta tambayeta shiru bata gansuba, Asiya ta zayyana mata abinda ya faru da kuma komawansu pharmacy.
Kai kaddararren pharmacy din yaki barin Asiya ta tafi. Asiya ta tambaya jikin farouk, ummi tace ya farka ya koma bacci. Toshi wannan wane irin baccine yakeyi haka? Tasan kaninta da son bacci kaman mage amma da dare ba safiya tangararas ba.
Kaman alluran baccine aka mishi. Waya mishi? Asiya ta tambaya cikin zafin nama. Wazaiyi Inba sojojiba, jiya su hamid sunce sunji harbe harbe da dare, to dama su asiyane? Lallai Asiya ta tuna taji farouk ya kwala ihu, kenan shi suka harba da alluran bacci, kenan tranquilizer gun ce? Asiya da hafiz suka kalla juna.
Aiko hakane, domin ummi ta cire abu a kafarshi kaman allura. To, yanzu kuma abinda su keyi kenan? To meyasa? Ya za ayi Asiya tasan dalilinsu na harbe mutane da tranquilizer gun. Ko ita da kyar tasha har sau biyu. Amma bata gaya ma ummi hakaba karta tadan mata da hankali.
Meke faruwa a amazon? Hafiz ne yayi wannan tambayan, domin yanzu kam sun kureshi, wurgama sahibarsa tear gas har saida ta sume! Ai inya rikesu ko sai sun gwammace CD ce ta takamasu. Ummi kam batasan meke faruwaba a amazon donba fita takeyiba, wama zai kara barinta ta fita?
Dole tasa hafiz da Asiya zama a pharmacy harsai tsananin ya lafa. Besides wannan zaiba hafiz daman sanin abinda ke zuciyar Asiya gamedashi kuma ya bashi daman nuna mata soyayya ba tareda takuran farouk ba.

Asiya ta kalla hafiz taga gashin fuskarshi ya fara taruwa bisaga yanda yake ajiyeshi. Ko tension nasa gashin fuskane? Hahhh very funny. Hafiz has been a real gentleman. Duk abinda take tunanin zai faru kwana biyar da suka wuce bai faruba. Tun bata sakin jiki dashi yanzu ta yarda dashi ta amince da bazai taba cutarda itaba.
Girki breakfast, lunch da supper duk hafiz keyi. Ita saidai kawai ta taimakada wanke plates wanda taredashi akeyi. In hankalinta ya tashi ya kwantar mata dashi. Saidai akwai abu daya dake damunta.
Abin yasa tayi kokonton tsayawarta daga ita sai namiji a wuri daya. Da bai faruba, da bata damuba. Amma wani abin mamakin shine, kaman abin bai faruba. Bawai don basu magana ba, kwana biyar da sukayi a pharmacy yasa sun kara sanin juna sun kara shakuwa da juna, kuma sun kara fahimtar juna. Amma wannan abin tsit kakeji. Kodai ta mishi magananne? Kai abinda kunya.
Lokacinda Asiya ta sume, farkawanta keda wuya sai taji wani al'amari na daban. Iska na biyu da hafiz ya hura ta bakinta ya farfadoda ita amma hafiz bai saniba don bata nuna alaman ta farfado ba. Dalili kuma shine, Asiya na jiran yaja baya ta mike sai karajin tayi lebbanshi a nata, sun manne yana hura mata iska.
Tabdi! Me hafiz keyi mata? Kiss?!!! How dare him! To bazai bari bane...ta shake da iska ta fara tari. Taso taci kaniyanshi amma sai taga kwalla a idonshi wanda yasata manta da hukuncinda zata mishi.
Asiya ta kara kallonshi, yasha bata saniba ne shiyasa ya boye zancen? Tasan ya ceci rayuwarta amma dole saita hakanne bayan akwai hanyoyi, ko zai ce mata shine kawai hanyar daya sani? Abin naci mata zuciya gaskiya ya kamata ta...
"Wow, say your mind baby, wannan irin kallo". Hafiz ya lura Asiya nata kallonshi saidai kaman tana tunanine kafin ya ankara wani kallo mai kaifi yaga tana harbinshida. "Gashin fuskarka yayi yawa". Hafiz ya tsura mata ido. To mai yakeso tace? Tana zargin yayi mata kiss lokacinda bata cikin hayyancinta?
Tunda shima ya boye ba sai kowa yayita rike asirinshiba. Yasan abinda yayi, amma baisan tasan abinda yayi ba. Ita kuma sanin nacinta danye wallahi. Amma bari ta gwada wannan. "Dama ka iya bada first aid?"
"Of course, training din danayi na military da aerospace...".
"Wait! Military!"
Hafiz ya shiga military har ya kai matsayin major sai kuma iyayenshi suka bukace ya bari. Ko a camp ya hora sojoji da dama kuma horonshi ba sauki. Dagewa da zafin nama da karfi da dangana sune motto dinshi kowa ya sani. In kana a platoon dinshi ka shiga uku amma kuma sune the best platoon ever.
Ba karamin hasara military tayiba da yai resigning. Haba that explains a lot. Asiya ta tuna taga idanunshi sunyi duhu lokacinda aka harbosu. An motso tsohon soja kenan, ta fara murmushi.
"To miye kike murmushi?" Oh! Ashe murmushin ya fita fili. Asiya ta girgiza kai. "Kinga kaman a filin yaki in opponent dinka yaji ciwo koya sume, you have to take care of him. Shiyasa akeyin program din first aid wurin training din sojoji.
"So.....wane irin first aid ne akeyi a training din?" Asiya ta fara kai harinta. Ya dangantane da irin ciwonda mutum yaji. In mutum ya samu injury a kafa ko hannu za a iya sa bandage a daure wurin don tsayarda jinin daga fita. In kuma is a harsh situation ba bandage, sai a sa belt a daure wurin ciwon.
In kuma mutum ya fada ruwane, dukda suba marine ba but ana koyarda swimming just incase of such situations, ka jawo mutum daga ruwa ka juyashi ta gefe tareda bude bakinshi ka dan daga kanshi don iska ya shiga hancinshi da neck donya turo ruwan da mutum yasha waje. In kuma kaci guba by mistake.... "Infa mutum ya sume?" Ta turo tambayan dake ci mata tuwo a kwarya.
Anan abin ya kasune kashi kashi. Inya sume ta fadawa ruwa, ana pumping ruwa daga kirji. Sai mutum ya aza tafin hannunshi akan kirjin mutum, yasa dayan hannunshi akan hannu na farko ya mikarda kafadunshi don suyi nauyin da zaisa idan mutum ya danna kirjin ruwa ya fita.
Na biyu kuma inya sumeta hanyan inhaling poisonous gas, to a fita dashi wurinda zai samu enough ventilation don air yana neutralizing gas din da mutum ya shaka. That is yana kashe ma gas din karfi. Hafiz na murnan yaga tana getting interested a bayaninshi, ita kuma kanta ya harba yayi sama gabadaya.
What!!! Yasan da wannan amma ya dauka dayan technique (hanyoyi)!!! Meyasa zaiyi haka? Waya bashi ikon tabata hakanan da sunan cetonta? Ta tsani samari masu son taba jikinta kaman sun biya sadakinta. Shiyasa tayi kaca kaca da gadafi, yanzu wannan shima?
And she almost thought ta samu miji ashe hanya daya ta kwaso su. Ya ilahi, wai meke faruwa da samarin now a days ne? Sai son bin haramun bayan ga halal suna gudu. Mistake dinshi kenan, eh na tabata ba. Kuma sai tasa yayi regretting abinda yayi mata.
Hafiz ya lura fuskar Asiya ta canza. A zatonshi tana sha'awan first aid ne shiyasa ta tambaya, amma yanzu yaga abinba haka bane. Yanayinta ya canza gabaki daya, harma kumburin haushi takeyi. Waya bata haushi? Kome ya bata haushi?
Ya koma baya tunanin abinda ya kawo haka. Ya tuna tayi tambayan first aid, kuma ya tuna tambayanta ya tsayane a idan mutum ya sume ya za ayi? Ya tuna ya bata amsa biyu ne kacal, na farko she was okay with it amma yana bada na biyun ya lura nan take yanayinta ya sauya.
Meya canzarda yanayin? Wani tunani ya fado mishi. Is it possible tana tambayanne don ta farka daga sumanda tayi kwanakin baya taga abinda ya mata? To amma a lokacin bata nuna komai ba, besides taimaka mata yayi ya ceto rayuwarta ba wani abu...
Amma ai ya bata options na taimakon wanda ya sume har biyu, ta kuma hanyan gas dayane ya bata. Gashi ta nuna fushin a zahiri lallai tasan abinda ya faru. Ai gwara a gyara zancen kafinta tayi mishi mummunan fahimta.
In kuma hakan bai tadarda wanda ya sumeba, in severe situation, sai ayi mouth to mouth respiration. A Kwantar da mutum flat a kasa, a matse mai hanci da yatsa biyu, a bude bakin mutum da dayan hannun, sai a shaka iska a hurama mutum a baki. Ayita yin haka har sai iskan ya shiga cikin lungs don ya kore gas din cikin gaggawa.
Ya Allah! This is a relieve, wai! wai!!! wai!!! Zuciyarta ta lafa daga tafasanda takeyi. Don da baiyi wannan bayanin ba tana nan tana kunsa yanda zatayi fata fata dashi, dukda bata sonyin hakan. Asiya ta kalleshi cikin tausayi da kauna. Ashe bawan Allah ya tsorata dayaga ta dade bata tashiba.
Ita kuma gata nan tana tunanin yanda zatayi watsi dashi. Kai misunderstanding baida dadi. Allah yasota batayi taking action da wuriba. Da yanzu itace take nadama alhalin bawan Allan taimakonta kawai yayi.
Ba karamin relieve hafiz yajiba dayaga yananyinta ya dawo daidai. Wannan shine tsallake rijiya ta baya. Ai sai ayi hankali from now on. Allah yasoshi da yayi rashi babba. Asiya tayi murmushi ta shige cikin boss office.
Hafiz ya ciro wayarshi ya duba yaga messages da yawa amma baiga message din dayake son ganiba. Yayi typing ma wasu reply, yayima wasu message ya maida wayan pocket.
Aida Inna lillahi farouk ya tashi daya tsinci kanshi a gidansu ummi. To, a karshe dai ya zama faisal mai zama gidan budurwarshi, kilama gwarashi farouk din tunda bai sanar da ummi komaiba. Tun daya farfado jiya ummi mistreating dinshi takeyi.


Duk abinda yayi ya lura haushi yake bata. Baya birgeta ko kadan kuma abin ya dameshi. Yayi yayi ta gaya mishi me yayine taki saidaima yasha bakar magana. Har saida ya dauka abin a hannunshi ya labe wani lungu a gidansu ya boye yana jiran tazo wucewa ya far mata don hanyan wucewartane.


Karyo kwanan keda wuya sai ya fito ya gaje mata space har saida ya kaita bango. Bayan ummi na haduwa da bango, ta lura ba wurin gudu kuma. Ta kalla fuskan farouk ya hade gira, kallon dayake mata mai kaifi, fuskarshi ba walwala.


"To menene?"


"Talk."


"Bani hanya."


"Tell me your problem?" Butakashin can, itace ma keda matsalan.


Ummi tayi banza dashi ta hade rai ta juye fuska. "Gaskiya ya kamata ka tafi amma kuma waya san halinda zaka shiga inka fita. Hala ka sake dawowa a sume. Farouk tell me something, zaka iya hakura da rai?"


"What?"


"Is a simple yes or no question."


"Ban gane in hakura da raiba."


"To ai hausace na maka, ba wani yareba. In badai so kake rayuwanka ta salwantaba, bani hanya." Murmushi farouk yayi ya kalleta da kyau. "Are you threatening me?! Ummi wannan rayuwar da kike barazanar halakata, ke zakifi kowa nadama da kewanta saboda takice, my heart belongs to you, na tafi."


Ya juya ya wuce ya barta cikeda mamaki. What!!! Did he just proclaimed his love for her?!! To, wow! Tama rasa me zatace. Jiki a sanyaye ta koma daki.


Can taji hayaniya a tsakar gidansu. Gidan irin 4 corners ne daki na bin daki sai tsakiya filine. Dakunan dake kusada kofan fita sune dakunan samarin gidan, tanan ne taji hayaniyan ta daga labule kadan ta hango bukar yasha gaban farouk yana hanashi tafiya.


Iyayenta suka fito suka sa baki amma ina farouk yace gida basu san ya fitoba gashi yayi kwanaki sunce lallai ya koma. Dukda hadarinda ake gaya mishi yaki yace aishi cutar bata kamashi. To don cutar bata kamashi ai sojoji zasu iya kamashi, maman ummi ta zayyana me. Yayita kawo musu kabuki da ba'adin da dolene saiya koma.


"Toku barshi ya tafi mana, jiki magayi."


Duk suka juyo suka kalla ummi. "In ankifa?", farouk yace.


"To an gaya maka tafiyarka zata ragemu da wani abune saidaima ta karemu wallahi. Don Allah brother hamid bude mishi kofa ya fice ya bamu wuri musha iska."


"Aiko naji dazu a news ana cewa daga baddo zuwa territory street duk wanda aka kama a waje a saki wuta kawai. Gwamna ya gajida mutane marasa jin magana". Duk aka kallo hamid.


Farouk yayi shiru yana nazari, wannan gwamnan nasu ba kai gareshiba, zai iya aiwatarwa. Yanzu ya zaiyi? Sai kawai yace ya fasa ai sai sumai dariya. Hamid ya kalla bukar da ummi ya kyafta musu ido. Ummi ta fara danne dariyan dake neman kubucewa.


"Tunda manya sunsa baki zanma su mom waya in gaya musu abinda ke faruwa". Ya kada kai ya shige dakin bukar. Habawa shigewanshi keda wuya ummi, bukar da hamid suka rushe da dariya. Baban ummi yayima hamid thumbs up ya wuce tareda maman.


Da yamma duka 'yan gidansu ummi suka fito akasa tabarma da kujeru a tsakar gidan aka zazzauna kowa nata nashi harkar kaman yanda al'adar gidan yake. Ummi tazo kusada farouk ta zauna. Ya kalleta ta gefen ido ya maida kallonshi gasu bukar.


"I'm sorry."


"For what?"


"Mistreating you. Ba halina bane sai in an taboni."


"Mena miki?"


"Cikin wannan dogon baccin da kayi, kayi mafarkin ka aurenine?"


Aure kuma? Shi yama yi wani mafarkine? Kai, ko yayi bazai iya tunawaba. "I can't remember, why did you ask?"


"Kace bakaso ka farka daga mafarkin nan, sooo sweet". Farouk ya tsura mata ido.


Yasan ummice tayita kuladashi tun lokacinda suka tsinceshi a bakin kofan gidansu. To ashe taji mafarkinshi? Amma taji duka kenan? Don a mafarkishi ya sumbaceta kenan ma wannan taji?


Wasu mafarkai daya keyi Allah yanasa yasan mafarkine hardai in basuda dadi, to hakama wancan mai dadin, yadai san bai aura ummiba amma gashi tareda ita a matsayin matarshi a mafarkin. Shiyasa yake fatan karya tashi daga mafarkin. To duka al'amarin taji kenan?


Abinda kunya donko abokinshi bazai iya gaya mai mafarkinba balle kuma ummul aba'isin mafarkin. "Yeah mafarkin nayi kin zama matata."


"Hm in your dreams. Dama anan zai tsaya, mafarkin ba."


"Do you think it's impossible ki zama matata?"


Ummi ta kalleshi ta juye kai. Farouk ya bukaci yasan kari gameda wacece ummi. Ummi de 'yar rose city ce, a amazon aka haifeta, duk schools dinta a rose tayi. Tayi saukan al'quran. Tana gama karatun pharmacy ta samu aiki a Ahmed pharmacy inda ta haduda Asiya.


Shikenan zai sani? Yayi mata complaining. Yaji dadima ya samu wannan. Hakanan ya hakura da abinda ya samu.



Kamshi ya duka hancin Asiya zumbur ta mike zaune kan couch a boss office. Movie take kallo mai suna contagion. Lallai kaman abinda ke faruwa yanzu, ta suri wayarta, ta mike ta nufa kicin. Oh! Hafiz bai gajiya da girki, gashi saidai in baiyi girki ba ko'ina kamshi zai dauka.


Murmushi ya yayi mata, fuskarshi yayi shaving kaman yanda ya saba. Yana juya potato pancake a pan. "Um kamshi ya taso dani".


"Zauna inyi serving dinki, I know you are hungry". Wayarta tayi kara ta duba mom ce, ta gama magana da iyayenta ta katseta sai kuma wayar ta sake yin kara. Hafiz yazota gefenta rikeda da pan da spoon yasa mata snack kan plate. Diba wayarta taga farouk ne, suka gama maganansu ta katse wayan. Hafiz yayi serving kanshi suka fara cin abincin.


Asiya tace mishi yau bata son heavy food shine yace he will surprise her ya girka mata wannan abincin. Cin abincishi na burgeta kullum cikin kamala da natsuwa, so neat. Dole itama ta dan dinga gyarawa don inda ace baya wurin irin lomanda zata dinga aukawa ba a ko magana saboda dadin abincin.


"Haffy". Suka kalla juna sukayi murmushi. "Yes sweety".


"Sisters dinka ba suyi aure bane?"


Imaan da khairat sunyi aure amma imaan na Washington tanada 2 kids, meena and yusrah. khairat na newyork, tanada da, Abdulhakeem, while zakiyya and raihana suna school a Riyadh gun grandma, maman babansu. Both of his sisters larabawa mazaunan U.S.A suka aura.


Hafiz ya kalla Asiya cikeda kauna dajin dadin kasancewa tareda ita "Baby, tell me more about yourself".


Asiya anan rose aka haifeta, tayi karatunta anan both islama da boko. Tayi attending rosey university ana kiranshi RU, inda ta karanta pharmacy bayan ta gama ta samu aiki a Ahmed pharmacy. Abokin babanta keda pharmacy din.


Asiya ta taso ita bamai surutuba sosai kuma ba shiru shiruba sosai. Gatada kamun kai hadeda kunya, ga jin tausayi tareda kulawa. Shiyasa patient in sunzo siyan maganin sunfi son su ganta, gata da gane yanda zata bi dasu su gane aikin maganin da yanda zasu shashi.


Dangi sun yaba da halinta na son gaskiya da yin adalci. Mutumce me son kyauta da taimakon marasa karfi. Koda yaushe inta karba salary dinta rabashi take gida uku. Na farko nata, na biyu iyayenta, na uku marayu.


Duk lokacin azumi, tana siyan kayan abinci ta kai orphanage, gidan marayu. Tana taimakawa masu karamin karfi iya yinta sannan tana taimakawa yara marayu da kudin makaranta.


"Masha Allah! Very impressive my love. Ban sha akwai sauran mutane irinkiba. Tell me your likes and dislikes".


Rikon daraja da mutuncin mutum dana gidansu. Hakuri da tawakkali a kowane hali mutum ya samu kanshi. Rikon amana da yawan bada hakuri da yin nadama in mutum yayi kuskure. Asiya nason mutum mai fara'a da murmushi daban dariya da natsuwa da kawaici.


Asiya ta tsana mara trabiyya da tsoron Allah. Ta tsana karya, yaudara da kwadayi. Ta tsana mutum mai shaye shaye, bin mata da son taba mata. Ta kuma tsana mutum mai saba alkawari, da kin daukan laifi sai ganin laifin mutum. Ta tsana mutum mai hayaniya da kin sauraron mutum, ta tsana chachan baki da musu.


"Wow! It keeps going this list of yours. So what did you think of me?" Asiya ta kalleshi harda karkace kai kaman tana tunani. "Handsome." Suka kwashe da dariya.


No seriously, hafiz kyakkyawane abinda zaka ce kenan daka ganshi. Amma idan ka lura ne sosai zaka fara gane shi wanene. Daga kalamanshi Asiya taji gaskiyanshi kuma taji ya kwanta mata a rai. Bata taba jin haka akan kowane samarintaba saishi.


"Wow my asiya, thanks a lot".


Har kewanshi tayi kafin zuwanshi pharmacy, bayan bata taba ganinshiba physically. Yana burgeta da kamalanshi da imani da tsoron Allah. Don sai mai tsoron Allah zai zauna da mace daga shi sai ita har kwananaki da yawa ko kalaman banza bai taba hadasu ba.Tsaftanshi na burgeta don kullum yazo kusada ita kamshi turarenshi mai dadi ke tashi. Tana kaunan yanda yake kallonta...


"How do I look at you sweety?" Tayi murmushi a sadda kai, can ta dago suka hada ido. Wani lallausan kallo yake mata mai cikeda begenta. Sai idanun su dan kankance su lumshe. Har wani yarrrr electric shock takeji inya mata kallon.


"Love, you are the best thing that happened to my life. I love you wholeheartedly. I wish you return my love a thousand fold. My life is always to serve you my queen".


Wayyo meyake cewane? Kwalkwaluwarta ta dauka charging. Itace abinda yake so a rayuwarshi, ya bude mata zuciyanshi gabaki daya, kuma yana fatan zata maida mishi da martani sau dubu, kuma rayuwarshi ya mika mata, itace sarauniyarshi?


Murna ba a kirga adadi a cikin zuciyan Asiya. Lallai lokaci yayi, ai ita ko a CD era dinnanne hafiz yace zai turo falillahil hamd. He's qualified a million times.