Chereads / TA ISO / Chapter 15 - BABI NA SHA UKU BAYYANA 1

Chapter 15 - BABI NA SHA UKU BAYYANA 1

Ita wallahi ta gajida kaya daya, waiya akayi ba su ajiye reserve ne? Infa wani abu ya samu kayan a lokacinda suke aiki? Gaskiya ya kamata a gyara. Zaune kan couch a boss office, Asiya na sanye da hijabinta tana jiran kayanta su bushe.

'Hey babe'

Sako ya shigo ta thisapp. Seda taji kirjinta ya bada dam. Lallai in CD bai kashe taba, hafiz ya kasheta. Wai yaushe yayi tasiri ne a zuciyarta haka? Inda so samune ma taji muryarshi. Da ummi tana wurin data rankwashi kanta, tace tana zubarda ajinta. Hafiz yana cewa he's a goner ai itace goner for sure din.

Kallon message din take tayi tana murmushi. Oh! ashe bata bashi amsaba.

'Hi'

'U free?'

'Nope'

'Plzzzz'

Lallaima wannan, to ai kayanta basu busheba, koda tana sanye da hijab ai ciki ba komai ya za ayi ta iya video call dashi a haka? Ta kalla hijabin me kaurine amma inaaa bazata iyaba.

'May b later, but can we chat'

'Oky, gud enof, hope all is well?'

Kewa ya isheta how can all be well? Sakonninshi na shiga tana kara jin dadi. Wai tsaya, dama inka samu wanda kakeso haka kakeji? To wai yaushe ta fara sonshine haka? Ko ganinshi a zahiri batayiba amma ta kamu haka, ita kam ta tashi daga goner ta zama gone. Gone in 60 Seconds, sunan wani movie.

Wannan karon ta bashi labarinta mutan gidansu, karatunta, aikinta da yanda ta makale a pharmacy din. Yaso yayi wani abu akai donta samu ta koma gida amma tace karya damu iyayenta na iya kokarinsu na ganin sun dawo da ita gida nan bada dadewaba.

'Asiya kina kusa?'

'Ummiri, gani'.

'Baby, idanuna sun hango mini the most beautiful face I've ever seen, kunnuwana sun rera min sauti mai dadi a sanidiyan jin muryarki, zuciyata ta buga kidi mai shiga jiki lokacinda nayi magana dake, jijiyoyin jikina sunyi dumi domin kalamanki sun ratsa ko'ina'.

Asiya ta dafa kirjinta dataga kalamanshi. Har wani zufa zufa takeyi, oh Allah ya so ta chat ne ba video ba da tayaya zata boye fuskarta? A haka ma kunya ya baibaiyeta balle in yana ganinta. Wani tiririn dadi ya cika zuciyarta ta rufe fuska tana murmushi.

'Give me a chance to prove my love for you sweety'.

Amma da wasa yakeko? Ai she's all his. Wane prove kuma? Aiya gama aikin handsome, hafiz handsome dinta.

'My love have no boundaries when it comes to you Asiya. To protect you i'll give my strength, to love you, i'll give my hrt, to be with you forever i'll give my soul'.

Wayyo dadi kasheta, koya sumar da ita, ko kuma kawai de ya barta raye ayi da ita, wadannan irin sweet words din, babu wanda ya taba mata irin su a duniya nan. Ta jujjuya a couch, ta kara karanta chat din sau kusan uku zuwa hudu.

'Who ever made ur hrt tough, I'll soften it, I promise to be truthful to you all my life. Inaso duniya tasan cewa ke tawace, inaso kisan cewa ke tawace har abada. Kowane dakika na rayuwata sonkine ke kara shiga zuciyata. Kowane minti nayi spending dake, shakuwarki ke mamaye jikina. Kowane awa nayi away from you, kewanki ke addaban zuciyata. I want you to be mine, my babe, my queen, my love'.

Hawaye suka gangaro kan kumatunta, please come take her she's all yours. Ta zama tashi har abada. Ta rufe bakinta murmushi ya bayyana a fuskarta tanata karanta sakon, farin ciki baya misaltuwa. Zuciyarta ta kwanta lamo tana jin dadin kalamanshi. Idanunta suka lumshe, a karan kansu hannayenta suka fara typing, ta kalla send option zata taba.

'Karki kuskura!'

Hmm waye wannan kuma? Taga ashe ummice, ai harta manta da wata ummi a wurin.

'Hala dashi kiketa chatting wannan irin shiru inata sending message ba amsa?'

Sai yanzu hankalinta ya dawo daga duniyan soyayya ta duba messages dinda ummi ta turo.

'Har yanzu shiru dad dinki bai daukokiba?'

'Dakin yarda wallahi mu kawo ki gidanmu'.

'Waime kikeyine shiru ba amsa?'

'Asiy ko kinyi baccine?'

Murmushi Asiya tayi, lallai hafiz ya kara tafiya da tunaninta. Ta kalla message dinshi tayi typing reply tayi sending mai, ta dawo kan ummi.

'Ba bacci nakeyiba, kuma abinda yasa dad bai iya turo an daukeniba saboda bold street restricted area ne. In kikaga bodies saikin ji kaman ki sume saboda yawansu. Anata kwashewa amma they are still too plenty'.

'Allah sarki, zan gayama babana, zaisan abinyi'.

'A'a ummi bar shi kawai in kinga mutanen daketa trying akaina you'll be surprised. Don't worry please'.

Yaushe zata bari ummi ko 'yan uwanta ko wasu su kamuda wannan cuta daba magani? Kawai saboda ita kadai dayawa su salwanta rayuwarsu, a'a wallahi ummi tayi hakuri harse sauki daga Allah yazo, wanda taketa addu'an yazo nan bada da dadewaba.

Kallon wayan hafiz yakeyi kaman bazai rabuda itaba. ko kifta idanu bayayi. Can ya lumshe idanu farin ciki bayyane cikinsu ya fara murmushi.

'I promise never to give my hrt to anyone again but with u, am more than willing to try'.

Call ya shigo amma inaaa su handsome ana tsakiyan birnin soyayya. Wayan dake hannunshi tayita ringing harta mutu ta sake ringing sannan ya dawo hanyacinshi. "Yeah?"

"Handsome, ya kake?"

"I'm good, who am I speaking with?"

"Shahid Ahmed, your one year course mate at aerospace NASA?".

NASA Community College Aerospace Scholars (NCAS). Course dinda yaje U.S yayine akan yanda ake sarrafa space jet da tukashi a space, wato wajen duniya. Abu daya yakaishi daukan course din, gano yanda zai hada space technology of jet mechanism da normal jet da aeroplanes, wato yanda zai hada fasahan speed na jet mai fita daga duniya ya gina jirgin sama mai gudu sosai.

Anan ne ya haduda shahid suka gaisa, tarema suke daukan lectures na course din daga baya daya samu abinda yazo nema, hafiz ya tafi abinshi. Shekara daya kawai yayi a course din. Dama sun karba lambar juna amma basu taba tuntubar junaba.

"Yeah, shahid, long time, how's it going?"

"Good, na shigo dazzle ne saboda rose ba a shiga city din, I had to drop here and am just looking for company, if you're not too busy?"

"Of course I am. Just joking, kana inane?"

"Hahhh na sauka a glitters, but I can come to you. Where you at?"

"At work, why ka sauka glitters instead of kazo gidanmu?"

"No haba de...".

"Ko gidanmu yama kadanne?"

"Noooo hahh haba de....."

"Look shahid, pack your belongings I'll arrange for you to be transported to handsome estate, at my villa. If you refuse nima bazan gankaba".

"Handsome kenan, toba matsala, thanks".

Hafiz ya katse wayan ya kira abbas yayi arranging ma shahid komai kafin ya koma gida.

Shahid na zaune a jeep grand cherokee SRT8, motar da hafiz ya turo daukanshi ya tuna zancen da suka yi da mom dinshi ta waya kafin ya baro Washington D.C.

* * * *

Akwatin shahid dauke da kaya ya kulle yaja trolley sai wayanshi tayi kara. Yana tsaye a dakinshi na Washington, ya dauka wayan daga gefen gado yaga mom dinshi ce.

"Shahid honey, thank Allah na sameka yanzu, hot good news I tell you". Ya murmusa sanin mamanshi da zumudi take.

"What is it mom?"

Nan fa take shafa mishi abinda dad dinshi yake niyyan yi. Hadashida 'yar abokinshi Asiya, aure.

"Aure kuma!"

Sosai kuwa domin babanshi ya yaba da hankalin yarinyar shiyasa yake kama mishi kafanta. Kuma gaskiya in harya aure Asiya yayi dacen mata mai kirki, tausayi, addini, kula da sanin mutuncin mutane. Gata kyakkyawa, son kowa kin wanda ya rasa. Babanshi yace zaiyima abokinshi magana muddin yarinyar ta dawo gida...

"Wait tana inane?"

Pharmacy din babanshi, ai nan take aiki, pharmacist ce.

"Ban katse miki hanzariba amma batada wanda takesone?"

Shigowar sakon hoto ya bashi amsa. Ya duba message din, nan fa ya tafi. Pretty face ya gaisheshi, Asiya na murmushi dimple dinta ya lotsa idanunta kaman tana hararan wandaya dauketa hoton. Tana sanye da atamfa sapphire blue, da stripes din golden a jiki, fitted gown mai dogon hannu yama jikinta daidai. Mayafinta golden ta rufe jikinta dashi, ya sauka zuwa cinyarta.

Shahid ya maida kallonshi zuwa ga bakinta, lebbanta sunsha pink lipstick sunata kyalli a hoton. Siraran yatsunta na sanye da golden zobe, Wuyan hannunta daureda sapphire blue agogo. Golden bag rike a hannunta, chains din jakan ya zazzago. Kyawawan kafafunta sanye da golden shoes. Wow, yarinyar ta hadu fa.

"Hellooo, sweetheart kana nan kuwa?"

Yayi mamakin kanshi daya tafi haka ya manta ma yana waya da mamanshi. Yayi murmushi ya shafa kai. Gaskiya yarinyar is gorgeous in her own way. Zaiso yasanta, ya ganta ido da ido sannan ya yanke hukuncin intayi mai.

"Yaka ganta?"

"She's beautiful mom, but I want to meet her first".

Kaga halin 'ya'yan zamani, a bari tayi sanyi shike kawo rabon wani. Amma zata bishi a hakan tunda ya yaba da kyaun yarinyar.

"One more thing, kadaka nunama dad dinka kasan maganan. Kayi kaman a lokacinda zai gayamane kasani. Banason ya hau kaina dana cika zumudi".

"Don't worry mom, I will comply with you".

* * * *

Ciro wayan yayi ya kara kallon hoton asiya, murmushi kadan ya bayyana a lebbanshi. Ya daga kai yana kallon waje ta windon mota.

Manya manyan bishiyoyi masu inuwa sun baje a gefen titin shiga handsome estate. Jeep din na karasowa ta tsaya gefen wani katafaren golden iron gate. Security sukayi check up suka gama, akaba direba pass ya saukarda glass kasa ya karba ya dago glass din ya tuka motan suka wuce cikin harabar estate din.

Gate na villa din low gate ne daga gaba filine mai fountain a tsakiya sai gabada fountain din wani gagarumin gidan sama hawa biyune mai bala'in kyau tsarin gidan. Jeep na tsayawa wurin rumfar shigan gidan, abbas da masu aiki guda biyu suka taryi shahid. Masu aikin suka dauka akwatinshi kan trolley suka shiga dashi ciki.

Abbas yayi mishi sallama, bada suna da marhaban daga baya suka shiga ciki ya kaishi dakinshi tareda bashi hakurin hafiz bazai samu daman ganin shiba yanzu saida yamma inya dawo daga aiki. Shahid ya tabbatar mishi ba damuwa zaije zagayen gidan ya dan mike kafarshi.

Shuke shuke iri irine daga kanana zuwa manyan bishiyoyi, da wanda shahid ya taba gani da wadanda baima sansuba. Kukan tsuntsaye keta tashi daya karyo wata kwana me glass corridor, kana tafiya kana kallon waje inda akayima wasu duwatsu kwalliya da grass da flowers a jiki a tsakar gidan.

Kofa ta kaishi lambu mai cikeda kayan alatu, ya zauna a wurin shakatawa mai daukeda two seats da rumfar ganyen kwakwa mai bulbs zagaye dashi a sama. Lallai villan zillionaire din ya hadu. Kafin ya ankara masu aiki suka kawo mishi drinks da snacks, suka koma.

Dandana drink din keda wuya ya rufe idanu yana jin dadin drink din a bakinshi. Kai hutu akwai dadi fa, ya kalla lambun kaman ba a dazzle ba. Amma bazaiyi mamakiba dazzling city kaman kasan wajene ya hadu sosai, balle gidan handsome of course sai haka wurin haduwa. Gayen naja fa.

Dukda shahid baisan hafizba sosai yasan yanada mutunci da kirki ga bin gaskiya. Shiyasa bai musaba yazo gidan ya zauna kafin abude rose city. Wata kyakkyawar budurwa ta bayyana a gabanshi harse da ya dan firgita.

Sanye takeda peach abaya, bakin gyale datayi wrap around hijab karami da. Hannayenta makale da silver jewels, abin hannu da zobe. kafafunta sanye da bakin high hill mai kyalli.

"To inka gama kallon se inji meye result din".

Shahid ya kalleta da kyau ya gyara zama, ya ajiye wayanshi kan tebur. "Ke wacece?"

"Ni wacece? hmm, kazo gidan brother na kana tambayan ni wacece?" Tace cikin takama da nuna isa. Shahid ya tabe baki yana kallonta cikin iko. "Oh ashe ma gidan brother dinkine, ba gidankiba".

"To saime, ai dan uwanane kaifa?"

"Ni abokinshine, dama haka handsomes ke tarbar baki? Ko haka matan sukeyi? Don the way your brother treated me was superb. But I see that you...lack manners".

"How dare you! Kasanni kuwa? Da zakazo har gida kana cewa banda manners, you small piece of shit.....".

"Whoa, Masha Allah raihana, waya bato miki rai kuma kikazo nan sauke fushin akan babban bakon handsome. I'm pretty sure handsome bazaiji dadin jin abokinshi was insulted to the ground level by his sweet little sister.

Raihana ta dasama abbas idanu tana hushin haushi. Zata yi magana...

"Um um".Ya tsareta da idanu. Ta turo baki fuuuu ta wuce daga wurin. Abbas ya juyo ga shahid. "I'm sorry sir, baby sister din handsome ce, she's troublesome".

"Not to worry abbas, I know their lots".

Dark palo raihana ta shiga tana cika tana batsewa. Dark palo yaci sunanshi, yanada dark curtains, dark 3D flooring, dark center carpet, dark ceiling, dark cushions, har wallpaper din bango dark ne.

Mata tazo gefen raihana ta tsaya gefen kafadanta. "Mistress meya faru? Naga kina jin haushi. Waya bata miki raine haka?" Ko kallonta raihana batayiba tace ta fice ta bata wuri. Bayan fitarta raihana ta mike taje gaban windo tana tunani.

Ita raiha za a dinta gargadi sai kace wata karamar yarinya? Wai abbas nema zai gargadeta? Who is abbas? Who the heck is he dazai dinga mata gargadi. Ya ma isa? Ai duk laifintane, eh data sakan me jiki ba, dolene ya rainata. Meyasa ta bayyana mishi abinda ke zuciyarta game dashi?