Chereads / TA ISO / Chapter 9 - BABI NA BAKWAI SAKO

Chapter 9 - BABI NA BAKWAI SAKO

"The public have the right to know how to protect themselves against this disease, it is not getting better as we are made to believe. Please I appeal to the public to remain indoors as I am, that is the only solution to not contacting this disease, and also do not come close to any person having red eyes and cracked lips. Keep away from such person as far as you can because these are the newly symptoms of the disease, which is God sent because earlier the symptoms do no show at all. Haleel, from high sky".

Shiyasa take son high sky t.v, ba ruwansu gaskiya suke gaya, shi kuma yasa sukayi makiya da yawa. Dukda haka basu gazaba saima abinda yayi gaba. Asiya ta canza channel.

* * * *

Iska ya bade Asiya yayi sama ya wuce, da kuranta lafa tayi jifa da icce gefen gate bayan tayi sanitizing dinshi. Da sauri ta koma cikin pharmacy tasa sakata tana nishi sama sama, ta feshe duk kanta daga sama har kasa, ta kuma feshe abin bude kofan, ta fincike mask da gloves tasasu a dustbin.

Ta zauna a reception ta rike kai. Kunna t.v keda wuya taji anata cekuce akan video da high sky suka fitar. Wayarta tayi karan shigan message. Ta zarota jiki a mace ta duba.

'Zanzo nida yayana mu kawo ki gidanmu yanzu'.

Hankalin Asiya yayi sama, tayi sauri ta kirata.

"Bakida hankaline ummiri, kina jin ana cewa kar a fita!?"

"Wallahi hankali bazai taba kwanciya inba na ganki a gidaba Asiya".

"Ummiri nafiki son in ganni a gida amma ya muka iya. Jiya saida na cire wani tsohon makale da small gate ya mutu a wurin. It is not safe please kuyi zamanku, beside dad yace zai aikoda troupe na soldiers suzo su daukeni, so karki damu don Allah".

Asiya ta rike numfashi tana jiran amsan Ummi. "Okay, naga video dinki, its heart breaking". Ajiyan zuci Asiya ta sake a boye kada ummi taji tasan tayi mata karya. "Mom tace bazai kawo min matsalaba da government, nace mata ban soki kowaba, halinda nake ciki kawai na sanar da mutane".

"Wanda zasu shiga uku da government ai sai high sky", ummi tace.

"Dama sun saba, last time kaman za a kulle station din amma mutane sukayita surutu dole aka barsu".

"Ai mutane garesu, mutane nason su soooosai in gaya miki".

"Zanyi wanka yanzu, se anjima, ki gaida su mama".

"Zasuji, later asiy".

Asiya ta jibge wayan kan counter ta dafa goshi.

Lebbanta sunata kyalli, leben sama kalanshi dark brown, leben kasa yayi pink, very attractive. Hancinta dai dai baiyi girmaba baiyi karamiba, idanuwanta sunyi kaman irinna 'yan China amma manya shape din kwai. Cikin kwayar idonta baki amma brown yayi highlighting dinshi so unique.

Tanata magana da wannan beautiful lips din... "Handsome". Aka kirashi. Wow! Ina babe kyakkyawa haka take boyewa a rose city bai saniba. "Handsome". Aka sake kirashi inaaa bai jiba. Lebenshi ya murmusa. Fine slim hands, kalla yatsunta so nice. Daga ganinta she's tall, ya Allah.

Hafiz na zaune a palonshi yana rikeda waya yana duba video din asiya. Tun lokacinda abbas ya nuna mishi video dinta yaji zuciyarshi na sha'awan kara kallo amma bai samu time ba sai yanzu.

Sai yanzu yake kara ganin kyaunta, yake kara jin muryarta, muryan data hanashi sukuni tun safe inya tuna sai yaji dadi a ranshi. Waima tsaya, meyasa yake jin dadi a ranshi? Shidai bai santaba, baima taba haduwa da itaba, halama tanada saurayi.

To yama za ace wannan beauty din batada saurayi? Aiko da saurayin ba abinda yasha mishi kai saiya..... Meyasa yake tunanin haka? Shifa mata basuma a tunaninshi, tun waccan budurwan. To ya akayi wannan ta shige ta gaje ko'ina? Wow! Is he inlove?

No no no he's not, its just infatuation, shine abin. Ya za ayi ya fara son wata dabaima santaba? Ai bazai yiwuba. Amma ya yakejin son kallonta da jin muryarta? Baya son wani tunanin akwai wani saurayin dazai zama obstacle tsakaninshi da ita kuma... To! ya sake komawa tunanin dai.

Abbas ya shigo yanata magana amma hafiz bai amsaba. Ya lura hafiz nata kallon video na asiya, budurwan nan dake rose city. Mamaki ya kamashi don bai taba ganin hafiz na kallon mataba komin kyaunsu kuwa saidaima shi yasha kallo daga wurinsu.

Ikon Allah har murmushi yakeyi toko lallai tunaninshi hakanne. Ba video din bane yarinyarce. Yarinyarce ta tafi da tunaninshi. Abbas ya ga wadanda suka fita kyau, amma ko kallo basu ishe handsome ba. Lallai tayi tasiri a ranshi. Tunda suke tare yau shekara 8 kenan bai taba ganin hafiz a yanayin nan ba sai yau, ko waccan ma ai bata sashi jin hakaba. This is a record kodai yayi video ne. Daga wayanshi keda wuya karrr idanun hafiz ne akanshi ta cikin wayan, yayi saurin sauke wayan. "Handsome, you called". Abbas ya wayance.

"And I know. What we're you doing?"

Yanda abbas yasan hafiz ko iyayenshi sai haka don kusan koda yaushe suna tare.

* * * *

Tsaye rikeda files a office, abbas ya duba ya hade gira. Kofa ta bude budurwa ta shigo. "Found the files raliya".

"Ko, to kakai mana".

"Inna kai mishi ba lallaine ya bashiba".

"To kai dama wa zaka kaima? Ai boss zakaba kawai".

"The thing is shiya kamata Inba saiya ba boss din, but bazai bashiba. Yaushe zai yarda asirinshi ya tonu".

"Amma fa kasani, cutafa za ayi ga mutuminda ya daukoka ya baka aiki. Ai ya gama maka komai. Ka shiga conference room din straight ahead kaje kakaima boss".

"Ko?"

"Sosaima. Ai bazaka dawo ka ciza hannun dake ciyar dakaiba. Ka tsaya a gaskiyanka dana sanka dashi, har akan hakan daka dunfaroni da zancen so na amince. Abbas ya murmusa ya suri files sai conference room.

Shigansa keda wuya saiya wuce kai tsaye wurin hafiz ya mika mishi files. Kewaye da tebur directocine su hudu sai manaja, ogan abbas. Manaja cikin mamaki ya kalla abbas wanda ko kallon shima baiyiba. Manaja ya fara wasi wasi, yana zurfin tunani.

Hafiz ya dago idanu daya bayan daya ya kalla directors din, sannan idanunshi suka sauka kan manaja. kirjin manaja ya bada damm. Bai san meyasa hafiz ke kallon shiba. Jingina baya da kujera hafiz yayi murmushi ya bayyana a lebenshi, yanata kallon directors biyu da manaja, kallo me sa mutum cikin tsarguwa, hardai in bakada gaskiya.

Tofa! Manaja ya fara zufa dukda a.c ne a dakin, kallon da hafiz yayima manaja saida yaji wani sanyi daga tsakiyar kanshi har yatsan kafanshi babba. "Lawal, Matthew, please leave the room". Muryarshi ma ta canza tayi kaifi. Lawal da Matthew suka kalla juna, suka kalla sauran directors da hafiz suka fice daga dakin.

"When did you discover this?" Ya wulla files din ta fuskar abbas. "Some minutes ago sir". Manaja ya dallo ma abbas harara, abbas yanata kallonshi ko a jikinshi.

"My own trusted employees wanted to over throw me". Ya shafa gajeren gemunshi yana sukinsu da idanunshi. A tsure suka kalla juna. Sunyi wannan abu a asirce, ya akayi ya bayyana kuma wandake karkashin manajane ya tonasu? Bakunansu kaman an makala glue, se idanu ke maganan.

Shin ina aka samu leakage dinnan? Kallo ya hau kan manaja. Duk sun kiyaye lamarukansu kuma abbas mutuminshine. Ya akayi yayi wannan sakacin? Sanin kansune in har hafiz ya kamaka da rashin gaskiya, ko cuta to kashinka ya bushe.

Banda zai tozartaka gaban jama'a, ya koreka aiki, bazai tsaya nan ba sai yaga a kasan nan ba inda za a daukeka aiki, sede kabar profession dinka kayi wani abin daban. In kuma kai wanine daya shakuda, kona kusa dashi, sannan kaci amanarshi, to zai nakasaka har karshe. Inda hali kabar kasan koka zama almajiri kanaji kana gani.

Hafiz ya barsu suka gama zancen zucinsu da kaduwan yasan abinda ke gudana a zukatansu sanna ya gyara zama, yana rola pen kan tebur. "You were going to be arrested for fraudulent, i step in for you with the power I have to see that you are free from the accusation". Ya dallo ma Khalid, manaja kallo me kada zuciya.

"I made sure that you didn't lose your house which will cause you your family due to your inability to pay the bank what you owe them". Ya harbo director ayo da kallo saida tsaigar jikinshi ta mike. "I made sure that your daughters were freed from their kidnappers and the kidnappers where caught and dealt with". Ya kalla director tanim cikin bacin rai.

Ya mike daga kan kujera ya shureta ta baya, ta wuce ta bugu da bango. Su uku suka kadu don basu taba ganin fushin hafiz ba. Abbas ya koma gefe ya linke hannayenshi a kirji. "Now, I am your target, bite the hand that feeds you comes with a prize". Hafiz na magana a hankali.

Kofa ta bude Chief security da guard uku suka shigo. Anan ne ido ya raina fata, ayo ya tsure jikinshi nata rawa. Khalid ko zufa kaman an bude pampo. Tanim kuma ya sadda kai kasa nadama yakeyi ba iyaka.

Waime yasaka shi cikin wannan abune? Kudinnan de akwaisu, a'a power hunger ne yakai shi ga haka. Son mukami ya kaishi ga rashi gaba daya. "Don Allah boss kamin rai". Jikin Khalid se rawa yakeyi.

"In maka rai, nina halicceka? Effective immediately, all three of you are removed from your ranks and will be taken in for questioning, we will meet then. Take them away".

Sunata kokawa da masu nadama da masu zufa suna rokon samun sauki, haka chief security da guards sukayi gaba dasu. Kofan na rufewa hafiz ya juyo ga abbas tareda jingina da tebur. "Your name and your unit". Abbas ya matso kusada hafiz. "Abbas mali, unit 10 manager's office".

"You can leave now". Har abbas yakai kofa.

"And abbas". Hafiz ya tsaidashi, Abbas ya juyo. "Thank you". Hafiz ya kalla cikin idanun abbas yana nuna tsantsan godiya. Abbas ya kada kai ya fice.

* * * *

Abbas ya dawo daga tunanin yanda ya hadu da hafiz, tun daga lokacin ya zama right hand man dinshi wato P.A, personal assistant. Kusan komai na hafiz ya sani saidai in hafiz din baiso ya saniba, koda abbas ma yasan abinda ba a so ya a sani, sai yayi kaman bai saninba. "I'm just ah...nothing".

"I have a job for you, and for you alone".