Chereads / TA ISO / Chapter 10 - BABI NA TAKWAS KEWA DA DANASANI ASIYA

Chapter 10 - BABI NA TAKWAS KEWA DA DANASANI ASIYA

* * * *

"Sis, nawa boots din suke? Kodayake ke zaki siyan min.....". Asiya ta katseshi.

"Eh eh eh tsaya daga nan yaro kanada kudinka kawo a siyanma". Farouk yayi dariya, ya kalla Asiya da kyau. Ta kalleshi ta matse tana taba wayarta.

"Sis are you serious at all? You must have thought ni wani gaulane dazan dauka makuddan kudi in damka miki ko?"

"Kai! Allah raba wanida mako".

"Allah raba watada kwadayi". Asiya ta suri pilo ta wurga mai, fittt ya gudu daga dakinta yana dariya.

* * * *

Murmusawa Asiya tayi tana kwance a couch na office din boss. Tana tuna lokutan da farouk ke addabanta. Pictures din wayanta take dubawa, ta dauka farouk yaci gayu zaije wurin budurwanshi.

* * * *

Sanye da shadda baka ta bugu ta fito da farin fatarshi, ya kafa hula, hannunshi daureda smart watch, ya dauka turare yana fesawa a gefen wuyanshi. Kofan dakinshi ta bude, Asiya ta kutso kai.

"Hmm mommy's boy, who's the lucky girl?" Ta daukeshi hoto da wayarta, ya wane poze(pose).

"Ruky baby, 'yar commissioner.....".

Asiya tayi tst tst tst da bakinta.

"To meye?" Ya kalleta ya bata rai.

"Oho de, haka zasu gama cinye maka kudi su barka heartbroken. All those rich girls that you are after ba. Kai baka daddara ai".

"Look sis, in bazaki gaya alkhairiba kiyi shiru...". Ta katseshi. "Ahh, ai dama zaka jawo min hadisi tunda baka son jin gaskiya".

"What if she's different....".

"A beg inta karyo zuciyanka don't even bring your sorry self to me complaining". Ya dire turaren da karfi kan bedside drawer fuuuu ya fice. "Inkaso ka zama jirgin sama ka tashi don fushi gaskiyane dole kajita". Ta daga murya don yaji.

* * * *

"Rouk kenan". Ta budo picture din da take murmushin dole wanda farouk ya dauketa.

* * * *

Hawaye na zuba daga idanun Asiya ta rungume pilo, gashinta mai santsi irinna fulani ga tsawo ga laushi, baki wuluk ya kware daga dirinta zuwa kan gado. Ta cacumi pilo tana kuka mai nishi. Farouk na tsaye yana kallon wayanta ya juyo a fusace.

"Sis, please kibar kuka hakanan. He's not even worth shading your tears for. Wawane wanda baisan abin kwaraiba. His lost ne wallahi. Forget about that idiot. Wallahi tunda baki da alhakinshi ko, seyaga abinshi. Useless person".

Farouk ya ajiye wayan kan dressing mirror yazo ya zauna gefen gado. Hannu yasa ya share gashin Asiya daga fuskarta. Jajayen idanu suka kalloshi, hawaye suka kara gangarowa. Ya sharesu da yatsanshi.

"Sis please, ki cireshi a ranki. I know it hurts amma Allah na nan". Damuwa ta nuna a fuskar farouk, giranshi hade yana shafa kan Asiya. "Amma.....yab...ya bari har saida.....aka...akasa rana". Zazzafan hawaye suka kara gangarowa. "To saime? Aka mayi aure aka watse ballema wannan, ai gwarama da ba ayi auren ba da haka ze dinga miki wulakanci, aiko da yaji jiki na rantse. Ba wanda ya isa ya taba min sister ya kwana kalau na rantse, sedeni".

Asiya ta kallo farouk, ya hade fuska ya kalleta suka kwashe da dariya. Ta tashi zaune ta goge hawayenta. "Mikomin wayana". Ya mike ya dauka ya bata. Ta kara kallon abinda wanda zata aura ya rubuta a message.

'Asiya this relationship is over, I'm not interested in marrying you any longer. Tell your parents the wedding is off'.

Tsiraran gashi nata yawo a gaban goshinta tasa hannu ta sharesu bayan kunnenta. Dagowarta ta hada ido da farouk. "Rouk, do it".

"THAT'S IT SIS!, that's how we do it. Shidin banza". Ya karbe wayanta ya kunna camera. Ya saitota. "Sis smile now".

"Rooouk ka bari".

"Come on, come on, kidanma rouk dinki murmushi mana". Asiya ta murmusa seda dimples dinta suka lotsa. Farouk ya dauka hoton ya ajiye wayan. "I am going to tell them now". Fittt ya fice daga dakin. Asiya ta jingina da gado kanta sama tana tunani.

MAI KWASAN GAWA

Rungumeda kai, abin duniya ya isheshi, zaune a lungu a palo, mutumin nan masu kwasan gawa wandaya ma dan uwan kwasan gawanshi duka harya mutu.

"Na shiga uku ni Usman".

Ya girgiza kai yana tunanin tashin hankalinda ya gano.

* * * *

Gama wayanshi keda wuya ya juya kalla gawan mutumin, kirjinshi na bugawa. Gayama ogansu yayi CD ya kashe hadi. Ogan yace ya nannadeshi yakai ramin birne gawawwakin CD victims, ya dago headquarters ya bada report. Amma harga Allah ya san shine ya kamashi da duka har yayi sanadiyan rasa ranshi. Yanzu yaya zaiyi, ya shiga uku ya kashe mutum.

Yana cikin mulmula gawan cikin leda yaga suit din hadi ya bule ta baya. Wato yanda akayi kenan iska ya shiga mai daukeda CD ya kashe hadi. Dukda haka shine sanadiyan kashe hadi, dabai far masaba da hakan bata faruba. Kan mace gashi ya kashe mutum.

Gaya mishi akayi hadi na neman matarshi tada, samira. Gashi dama neman sulhu yake. Shiyasa ya tuhume hadi shi kuma ya nuna mishi sai inda karfinshi ya kare wurin ganin samira ta zama tashi. Yo wayace ya saketa. Shine zuciya ta hau shi yayi aika aika.

Bayan nannade gawan ya tulata boot ya kaita bayan gari ya wurga rami tareda sauran gawawwakin. Yayi mishi addu'a daga nan ya koma headquarters dinsu. Yayi parking mota cikin garage ya fito hankalinshi a tashe, wurin sauri ya bige wani. "Kai malam haba....". Bai tsaya saurareba ya wuce dakin sanitizing.

Mutuminda usman ya bige yana tafiya kadan ya tsaya, ya rike wuya ya fadi kasa ya hau birgima. Mutane na ganin haka rudani ya tashi. Sai guje guje aka farayi. Iska ya taso daga wurin gawan ya bade headquarters din.

Fitowar Usman keda wuya daga kofa yaci karo da wani abu. Kallon kasa keda wuya yaga gawa, hankalinshi yayi sama ya matsa daga wurin a rikice. Duk inda yabi gawane. Mamaki da fargaba suka isheshi. Ba yanzun nan ya shigo nan ba komai lafiya duk mutane nada rai amma kafin ya shiga ya fito sai gawawwaki.

A firgice ya koma cikin headquarters din, nan ma yaci karo da gawawwakin wadanda yanzu ya gansu da ransu. Tabdi! yaushe annoban ta iso? To ya akayi shi bata kasheshiba!!? Ya sampe a guje ya bar headquarters.

* * * *

Yanzu tambayan itace, ya akayi CD ta iso headquarters? Suna daukan mataki mai karfin wurin sanitizing harde in mutum ya dawo daga kai gawa. Bayan kayi parking motarka a garage din sanitizing motoci, sanitizing gas yake bade motar, kai tsaye zaka wuce sanitizing room dake joneda garage din, gas ne zai badeka kafinka cire suit din nan ma. Akwai kofan fita daga dakin ta dayan bangaren, zaikai mutum cikin headquarters din.

To kuma duk yayi haka.....tsaya, wani mutum yaci karo dashi kafin ya shiga sanitizing room. To kenan shine ya karayin sanadiyan rasa rayuka da yawa!? Kai a'a duk yayi abin da ya dace, saidai in cutar ce yanzu bata jin sanitizer. Idanunshi sukayi ja, hawaye suka fado.

UMMI

"Yaya dai Ummi, lafiya?". Maman Ummi ta zauna gefenta kan kujera a tsakar gida.

"Um, mama nifa hankalina ya kasa kwanciya wallahi, saboda halinda Asiya ta shiga. In kika kalla news sai hankalinki ya tashi, don cutar kara yaduwa da daukan rai kawai takeyi".

"To ya kika iya? Saidai mu tayata da addu'a kawai". Ummi ta girgiza kai. "Mama nasan da haka amma banyi kokariba, da tun farkon abin na matsa mata munzo gida tare. Gaskiya mama, nayi nadaman rashin jawo wannan dogon gashin nata muzo".

"Uhm, Ummi kenan da abin dariya kike. Nide tashi kije ki gyara min daki".

* * * *

Ummi ta shigo office din asiya, shigowarta keda wuya kawai ta taka birki. "Subhanallah! dama haka kikeda gashi!?"

"Kai ummi! kin bani tsoro". Ummi ta iske Asiya tana kitse gashinta ta jawoshi ta gefen kafadanta. "Umm masha Allah, wallahi ina son gashi rayuwana".

"Dama zakiyi sha'awanshi amma wallahi damuwane". Ummi ta zaro ido. "Wane damuwa!!? Aini inason in ganni da gashi kaman me".

"Don dai ba a kanki yakeba".

"Inyita gayuna dashi, in wurgashi nan, in wurgashi can....".

"Kiyita riritawa, sarkin surutu, ummiri kenan".

"Meye kuma ummiri?".

"Ummi me riritawa, in bakin nan naki ya bude kaman pampo". Ummi ta murmusa.

MAI RAHOTO BADDO ROAD

Kuka, bakin ciki da danasani ya isheshi. Dayaji maganan ogansu daba hakaba. Tun yana karami yake da rashin ji, gashi yau rashin jinshi ya jawo ya rasa babban abokinshi sani. Zaune yake a simintin balcony yanata rusa kuka duk lokacinda daya tuna da abokinshi.

* * * *

Sani yana gyara cameranshi, yana goge kura daga jikinta. "Zamujene abu?" Mata kibabba shekarunta zasu kai 35 ta iskosu bakin kofa. "Kuje ina!? Kunajin ana cewa mutuwa ake tayi ko'ina."

"Mufa 'yan taurine."

"Eh, tauriko? Har oga ya bugo yace kada wanda ya fita fa, ABU!"

"Kadaki damu, zamu samo miki story." Abu ya sura key na mashin wayyo kudina, shida sani sukayi waje. "Karfa kuje". Ta bisu har waje tanata gargadinsu amma akunnen kashi gargadin ya fada tuni sun sampe a guje kan mashin.

Suka iso baddo road. "Mu fara daga baddo". Abu ya kashe mashin yana parking, sani ya sauka yana kalle kalle. Kwararan mutanene keta harkokinsu, sani ya saita camera ya fara daukan abu. "Daga nan baddo road yau safiyan litinin, tara ga watan Maris, dubu biyu da ashirin. Yanzu karfe....." Ihu da gudun mutanene ya katseshi daga abinda yake cewa.

Mutane sun kai hamsin suka rugo a guje kowa nata gudu ba hankali, wasu a take, wasu a murje, wasu a bige. Sani ya jawo abu suka makale gefen wani katanga. Duka mutanen sukayi saman layin baddo, wucewansu keda wuya abu yaga mashin dinshi a kasa. Yayi sauri yaje ya daga ya gyara mishi zama.

"Rola, rolata mubi mutanen can sauri". Abu yacema sani ya rola camera ya fara gudu gudu yana bin saman layi, sani na daukan hoton yana bin shi. Dambu sani ya fara daukowa a cameranshi. Ya kara zooming kawai sai yaga mutanene kwance a kasa. Harya fara tunanin me mutanen nan keyine a kasa sai ganin yayi abu ya ruga wurinsu a guje shima yabi ya tsaya nesa dasu yana daukan hotonsu ta video.

Duka mutanenda suka rugo saman layin ne a mace, gawa kan gawa. Hankalinsu yayi bala'in tashi. Jiki na rawa, abu ya fara magana.

"Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'in, don Allah a kawo muna dauki, mutane sai mutuwa sukeyi haka kawai. Ni....ni kaina duk gawane kewaye dani. T...to....".

Wata mata ta rugo a guje tabi gefen sani tayi wurin abu. Tana nishi tana kuka a firgice. "Yarinyata!, don Allah ku agaza mini yarinyata....". Sai kawai ta fadi a mace. Sani ya sulale ya fadi a mace. Abu ya rude. "Sani! SANIIIII!!". Ya dauka cameran yana daukan kanshi. "Don Allah jama'a a lura, ku zauna a gidajenku... Ni...nina tafi. Daga nan baddo road". Yana Kuka yana magana.

Abu ya rasa yanda zaiyi, sani abokinshi ya mutu mutus. Kawai ya balla da gudu ya isa wurin mashin dinshi ya dale ya buga ya fice daga baddo.

* * * *

Abu ya kalla kasan balcony, hawaye suka gangaro. Zuciyarshi daci take mishi. Me zai gaya ma iyayen sani? Ko ogansu wurin aiki da yayi gargadin kada a fita? Ya jefa kanshi cikin garari.

MOM DA LIMAN

Mom ta tadama liman hankali akan lallai yasan yanda zaiyi adawo mata da 'yarta. Farouk ma an dawo dashi, shima da ba asan inda yakeba a lokacin balle Asiya da ansan inda take. Liman yayita buge bugen waya amma abu ya faskara. Abokanshi wadanda ya bugama wanda ke military sukayita bashi hakuri saboda gaskiya bold street is one of the no go area tun farkon abin.

Ko gawawwakin da ake kwashewa sunyi yawa kaman karuwa sukeyi. Hadarine sosai zuwa wurin a yanzu, amma sunmai alkawarin ana samun sarari zasu tura a daukota. Inaaaa mom ta kara watsewa da masifa 'yarta tilo bai damu da itaba, ya za ayi ta barta wuri irin haka. Tayita kuka har saida farouk yazo ya kwantar mata da hankali.

Yafada mata ai inda Asiya take is safe, but hanyan zuwa wurintane danger din yake. Ina amfanin an fita dauko mutum daya an rasa da yawa? Komitin kwasan gawawwaki suna nan suna kwashewa kuma sunata kokarin ganin sun kwashe nakan titi don samun hanyan inda mota zata wuce.

A haka hankalin mom ya kwanta hartaba liman hakuri. Asiya tasha kira a waya harta gaji. Mom ta kuma fara complain Asiya bata son daga wayarta so take ta tadan mata da hankali. Nan ma farouk yayita lallabata da cewan tasan Asiya na cikin wani hali, karta azazzali Asiya da waya don duk sanda Asiya taga wayanta zatasha za azo daukantane wanda kuma ba haka bane.

Liman ya murmusa daya ga yanda dansane kadai ke iya shawo kan matarshi in ta birkice. How ever did he do it is a mistery. Don koda zai gaya mata the same words bazaiyi aikiba. Wato yaron yasan yanda yake lallaba mom dinshi his own way. Ya kalle su ya murmusa.

* * * *

"Mom kar a siya tin tomato nafison fresh ones..."

"Ai abin da yasa munada fresh tomatoes a garden."

"Eh but they are not plumpy and juicy."

"To sa dasu." Liman yayi sallama ya shigo palon mom ya iske mom da farouk suna list na foodstuffs, gefe zaune Asiya nata bankoma farouk harara in ya kalleta ya haskomata fararen hakoranshi.

"Dad, ka ganshiko yana tsokanana". Asiya ta tsaya gefen dad. "Yaushe ya tsokaneki, kede kin cika son takura mishi".

"Ai shine, I'm here minding my own business...". Asiya tayi kanshi, dad ya riketa. "Muje sweetheart kyalesu".

"Amma dad sunki susa sausage a list din kuma duk sanda nace asaka abu, sai wannan dan rainin wayon yace wai in inaso in siya da kaina bade a list dinsuba". Ta turo baki. Dad yayi murmushi kadan. "kyalesu muma muje muyi namu".

"Yawwa mom asaka parsley ko?".

"Hakane harna manta good boy". Farouk harda kallo Asiya ta gefen ido yana murmushin gefen baki. Asiya tayi fuuuu ta fice daga dakin. Liman ya kalla farouk.

"Better behave yayarkace".

"But dad....".

"Kyalesu, duk 'yan bakin cikine". Mom ta shafa kanshi. Liman ya murmusa ya fice daga dakin.

* * * *

AHMED

Kusan kullum sai Ahmed yayiwa Asiya waya don jin ya take, in akwai duk abinda take bukata a wurin ta dauka. Sannan yayita bata hakuri akan rashin zuwa daukanta saboda health issues. Asiya ta tabbatar mishi da cewa ta gane, ai lafiya yafi komai saboda haka karya damu kanshi. In komai ya lafa sai azo a dauketa.

Ahmed ya yaba da kaifin hankalin Asiya amma ba abin mamaki bane babanta ta biyo duk yaran liman haka suke da hangen nesa da hankali. Wani tunani ya shiga kanshi. Danshi, ya kusa dawowa duniya daga duniyan wata da sukaje a U.S NASA, saboda ma wannan epidermic dinne da tuni yazo.

Murmushin jin dadi yayi don yaga ya hado wani abinda za aji dadinshi, hardai in ya gayama yusrah balle abokinshi liman. Kuma fa zasu dace. Shi fari, ita chocolate brown, zasu haifo 'ya'ya masu kyau. Ina ruwan Ahmed harya shiga nashi shagalin.

Ga yarinya da biyayya da rikon amana, dubade yanda take rike mishi wuri tsakaninta da Allah kuma annoban nan baisa ta bar mishi wuriba. Gaskiya abubuwa na dawowa daidai zaiyi hanzarin sanarda liman kudurinshi.

* * * *

Office din Ahmed a kacame, takardu ko'ina a watse har kasa. Asiya ta shigo ta taka birki. "Meke faruwane haka?" Ahmed na zaune a couch yanata rubutu da note(Karamar computer). Ya dago yaga Asiya ta shiga gyara. "Dakin barshi, jamil zaiyi".

"Noooo its too rough uncle, ba damuwa zanyi".

"Are you not busy?"

"Nope".

Ahmed yayi murmushi ya cigabada aikinshi yana duba papers.

Ahmed na kwance a gida ba lafiya wayar asiya ta shigo. "Uncle, ina kwana?"

"Lafiya 'yar uncle kina lafiya?"

"I'm good, ya jikin naka?"

"Da sauki gobema zan shigo.....".

"No way, kaji yanda muryarka takene? Ka huta uncle don Allah, kabar min komai nidasu jamil har saika warware. In kuma ka matsa saikazo wallahi zanma aunty yusrah waya". Ahmed ya murmusa tareda girgiza kai. "Haba 'yar uncle, harda warning?"

"I know you uncle zakace sai kazo. Yi zamanka har saika ji sauki".

* * * *

Lallai Ahmed zaiyi suruka mai tausayi da kula. Aiko sai inda karfinshi ya kare wurin ganin Asiya ta zamo tasu. Ai samun yarinya kamarta da wuya a zamanin nan ga ladabi da biyayya ga shiga ta mutunci ga kunya da girmama na gaba, aita tara duk abinda akeso a samu a mace.

Ya murmusa. Gyara zamanshi keda wuya yaga yusrah na kallonshi. Ta zauna gefenshi a gado ta daga kai ta sauke, alaman 'me ake ciki?'. Ahmed ya zayyane mata duk abinda ke zuciyarshi gameda danshi, shahid da Asiya.

Murna ba ako magana wurin yusrah. Don farinciki, tanata zumudin yanzuma zata bugama hajiya farida, maman Asiya waya akan maganan. Ahmed ya tsaidata yace kyaun abin a bari se bayan wannan annoban...

Inaaaa ai a bari ya huce shike kawo rabon wani. Ai kawai gwara ayita yanzu... Ahmed ya tuna mata cewa 'yarsufa bata dawo hannunsuba. Ai duk zumudinta dai zata bari asiya ta dawo gida cikin koshin lafiya. Sannan ne ta amince, da kyar.