"Gwamna bakari na jihar rose yayi kira izuwaga mutane dasu hakura su zauna a duk inda suke don gudun cigabada yaduwar annobannan...." Asiya ta canza channel. ".....update on this newly disease known as cervix disease. With me is the director of NDCC Doctor john abraham, doctor please can you highlight us on this turn of event going on in the city", newscaster din tace.
"The national disease control center is on the move to find how to contain this virus at the same time finding an antidote as quickly as possible because at the rate this sickness is moving is very alarming. The start up point of the disease is unknown but the first case was reported to NDCC this morning from the general hospital of rose city, right now we are dealing with several cases around all hospitals in rose city", john yayi bayani.
"People will like to know how to tackle with the situation, because according to several reports we have been receiving, a person can contact this sickness by mere skin contact, or even by been around the person that dies from the disease, regarding to this reports the question here is that, is this sickness airborne?"
"To ai shine." Asiya tace tareda gyara zama. "The nature of the virus is definitely airborne, which is why face masks should be worn at all times, before we are able to find a cure."
"Tashin hankali, airborne disease is the worse case ever." Asiya ta canza channel.
Ansa dokan ta baci saboda a cewan wasu rahotannin, annoban wadda ba a san sunantaba ta ketare rose city, ta fara shiga makotanta, dazzling city. Ba a son aga kowa a hanya daga yanzu harse illa Masha Allah.
Tabdi! Kenan suna nufin baza a koma gidaba duk inda kake nan zaka makale? Asiya ta mike, ta ajiye remote ta haura kitchen. Abinci ta fara duba yawansu taga kwanaki nawa zasuyi mata.
Freezer ta nufa ta bude, akwai ferarren chips, doya da sweet potato cikin sealed nylon, ta kirga leda hamsin, jan nama ya kai kilo biyar, naman kaza guda goma, kifi carton biyu, ganyaye kala kala sunyi kankara cikin leda me kauri fari, ta kulle freezer.
Ta bude cupboard, madara, bourvita, Milo, Lipton, oats tins goma goma, packets din cornflakes da golden morn goma goma, bread leda biyar. Spices gasu nan birjik, man girki na roba a jere sun kai goma da tumatir na sachets, taje store, karamin buhun shinkafa uku, taliya carton biyu, indomie babba biyar, karami biyar, wow! Lallai uncle Ahmed na musu hidima. Ta bude fridge mai double doors, shakare yake da drinks da juices iri iri, bottled water, kwai mai gida shida crate goma, harda cheese. Yunwa ba matsala bace for now.
Saukowa daga stairs tayi ta nufa kantan magani tana duddubawa. Vitamins, antibiotics, gestid, maganin ulcer dinta, taga dentist brush da dettol ta dauka, packet na hand gloves da face mask ta cire wasu, wadannan zasuyi amfani. Ta shiga medicine store dake gefen reception, shakare yake da magunguna carton da yawa. Wayarta dake aljihunta tayi kara, ta fito daga store ta rufe.
"Mom! Farouk ya dawo?" Tace cikin fargaba.
"A'a asiy, dazu a news akace ansa state of emergency, Kuma ciwon nan har dazzling city."
Asiya ta saki ajiyan zuci. "Haka na gan."
"To abincin nada yawa nan wurinki?"
"Eh, uncle Ahmed ya shakare wurin da abinci, in kika gani kyace baki yake entertaining anan". Tana tafiya ta shiga toilet din kasa, taga yanada wurin wanka da sabulan wanki a cikin cupboard din bayin, ta fita ta kulle ta haura sama.
"To masha Allah. Babanki nata neman manyan mutanen daya sani a waya daga military don a samu ayi tracing din wayar farouk."
"Kai! Harna ji dan sanyi sanyi mom, Allah bada sa'a."
"Amin, kada ki tsaya da yunwa fa. Kuma ki kwantar da hankalinki don kinsan ulcer dinki zai iya tashi."
"Yes mom, karki damu dani, Insha Allah we will pull through this jarabawa."
"To ina zaki kwanta?"
Asiya ta shigo office din boss ta zauna a couch. "Mom, kadaki damu zan san yanda zanyi, ba abinda ze gagara." Kira ya shigo wayarta. "Mom I have to go, ana kiran wayana."
"Allah tsare minke asiy."
"Amin". Ta dauka dayan kiran. "Asiya kinji yanzu kuma state of emergency ne, Allah kizo gidanmu.....". Zuwa gidansu ummi ma ba option bane, gawawwakin dake tsakanin bold street zuwa amazon Allah yayi yawa dasu. Hadarine mutum ya kutsa ta cikinsu ai. Asiya ta murmusa. "Calm down ummiri, wannan irin zuba."
"Ke naga kaman baki damuba, nifa na damu da halinda kike ciki."
"Duk abinda ya samu bawa ummiri, mika al'amuranshi yake ga Allah, shiyasa kikaga nayi calm, inba hakaba a lokaci irin na rudunnan sannan mutum ya rude, aida sede a kwashi mutum kawai."
"Gaskiyane, ban taba jin tsoro a rayuwata irin wannan karonba. mutane kaman kwari ko'ina ka waiga a mace."
* * * *
Fitan ummi daga gate din baya na pharmacy keda wuya, taji Asiya ta kwala mata kira tasa face mask. Ta tura hannu cikin jaka ta ciroshi hannunta na rawa tasa. Ahmed yasa doka ta dole sai anyi amfani da face mask da hand gloves in ana hulda da magani. Saboda haka akoda yaushe ma'aikatanshi suna tareda su. Mutane nata guje guje, a kidime. Tana kai karshen layi taga gawawwakin mutane kwance ba wurin saka kafa. Ta sankare tana waige waige, can taga wani lungu ta arta a guje tabi ya kaita saman layin gidansu.
"Ummi!!!" Kirjinta na bugawa kidi kala kala ta juyo.
" Brother hamid! Meya fito da Kai?".
"Ke mukaje mu dauko daga wurin aiki. Baba yace muje muzo dake, gariba lafiya."
"Kai dawa?"
Wani saurayi yazo gabanta a rikice ya tsaya. "Muje don Allah tunda gata nan. Wai meke faruwane?" 'Yan uwantane sukazo tafiya da ita sai gashi sun ganta kusada gida. "Hmm, muje gida tukunna zan baku labari."
* * * *
"Yasu mom, injin dai kowa lafiya?" Ina lafiya ba a san inda dan uwanta yakeba. Yana rayene ko ya mutu duk ba a saniba. Gashi ance ba fita, kowa ya tsaya inda yake, to shi farouk ina yake?
"Ummiri, ba a ga farouk ba, amma za ayi tracking phone din shi."
"Inna lillahi, Ya Allah kasa a ganshi ka dawo dashi lafiya, oh! Wannan lamari duk ya watsarda jama'a."
"Amin ya Allah, thanks a lot."