An samu mace mace a sassa daban daban na jihar rose, gwammati ta sa a fara kwashe gawawwakin a haka rami babba a birnesu ciki. An hada kwamiti na kwasan gawawwakin har sun fara kwashewa tareda sa tufafin kariya daga daukan cututtuka. Zasu sa gawa a cikin ledan da aka tanadar musu, su tulasu a pickup su kai inda za a birne. kowane unguwa yanada group na mutane masu kwasan gawa.
komai na tafiya yanda aka tsara seda wasu mutane biyu zuciya ta hau suka fara rigima daga nan se dambe ya gauraye tsakaninsu. Daya na cikin rufe gawa a leda dayan ya tureshi ya fada kan gawan ta kwance. Wanda aka ture yana kokarin mikewa tsaye kawai dayan ya auka mishi suka fadi kasa yanata kai masa naushi a ciki.
Suit din wanda akema duka ba tareda saninsuba ta bule ta baya. Iska na korowa tabita kansu ta wuce. Wanda akama duka ya fara kaki yana taba wuya. Dayan mutumin yabar dukanshi yana zaune a saman cikinshi yana kallonshi a rikice.
Ya fara tambayanshi lafiya, don yaga baima taba wuyanshiba. Mutumin ya bar motsi. Hankalin dayan ya tashi ya mike tsaye cikin rudani yana jada baya yayi sauri ya ruga mota ya dauka rediyon magana yana bayani.
Mai chemist yana zaune a kulle cikin chemist dinshi ya gama sauraren ridiyo, suna magana akan a dinga shan vitamins suna kariya daga cututtuka duk dadai ba maganin cutar data kama mutanen rose city bane.
Aiko ya cakuma kwalin vitamin c ya tura a baki, a tunaninshi yayi rigakafin cutar. Chemist din na jone da gidanshine. Minti takwas da hadiyan vitamin c yaji kirjinshi na zafi, ya kama kirji ya murza ya buga, abin ba sauki. Yaji wani makaki a wuyanshi, ya rike wuya da kyar ya shiga tsakar gida ya zube a kasa rikeda wuyan.
Matarshi tazo shiga kitchen na waje ta hangoshi yanata kaki tayo wurinshi a guje.
"Lafiya mansoor!? Mansoor meya faru!? Na shiga uku". Ta fara kuka tana jijjigashi. Yabar motsi ta sankare, ta rude ta kwala ihu ta zube kasa.
NDCC(National disease control center) Rose city
Mata rikeda papers a hannunta ta fito daga lab tana tafiya cikin sauri, hankalinta a tashe ta iso office din assistant director ta ingiza kofan ya bude ta shiga. Yana tsaye yana jiranta.
"Sir! sir this is the result of the new samples." Assistant director ya karba cikin hanzari ya duba, can ya sake papers kan desk ya kalla matar cikin kaduwa. "I know, the cells have mutated, and the speed of mutation is alarming. Fifty cells per second!", Tace.
Hannunshi na rawa ya jawo waya ya nemo lamba ya kara a kunne. Matar ta zube kan kujeran gaban desk din. "Doctor john, a new situation has arise...."
A conference room suka taru, director, assistant dinshi, manager, H.O.D na lab, matarda ta kawo result din kenan, da wasu manyan likitoci su uku, maza biyu, mace daya. Kowa na zaune ana tattaunawa kan sabon matsalan data taso. Wuri ya kacame da surutu.
"Listen everybody, logical thoughts, NOW!" director ya daka tsawa kowa yayi tsit. "Sir, the mutation has caused the cell membrane to be tougher, this results in the virus resistance to the medicine we made earlier AB 19, which was administered to the virus cells which weren't mutated at that time.....", daya daga cikin doctors din yace.
"We have produce a new antidote which is stronger than the first one..." John ya katse doctor na biyu. "And this antidote, have you tested it yet?"
"It is in the process of experiment as we speak", doctor ta uku tace. "And who is conducting that experiment?" Idanun kowa ya koma kan doctor ta uku.
Kofan conference room ya bude, dukkansu suka waiga don ganin waya shigo, dan gajeren dattijo ya shigo cikin sauri sanye da lab coat, rikeda papers. Yazo kusada H.O.D, yayi mata rada a kunne tareda nuna mata papers din. Ta sankare tana kallonshi sannan tayi gyaran murya tareda karban papers din. Scientist din ya fita. Kallo ya koma kan H.O.D.
"Sir, the mutation speed is unmanageable. According to these results, the mutated cells reaction to the new drug known as AB 20 is not effective, due to the production of multiple defensive spikes...."
"Spikes?", john ya sake baki.
"Spikes, just like spears use in the olden days as defense mechanism, this virus counter attack with defensive spikes around the outer shell of the membrane". Kowa yayi tsit. H.O.D ta kalla dukansu, john se kada kai yakeyi cikin mamaki.
"The disturbing thing is, the more powerful the drug is, the more powerful spikes the virus produces".
"What!?", john yace cikeda mamaki.
"Tashin hankali", assistant yace.
"How is that even possible!?", john ya tambaya.
"The most disturbing thing is, the spikes produced, shoots out to attack healthy cells of the subject".
"Impossible", assistant yace.
"Meaning?", john ya tambaya a kidime.
"The infected subject when ingested with the drug AB 20, will die faster because the drug is more powerful than AB 19 the previous antidote, due to the fact that the virus attacks back if stronger medicine is ingested. The earlier version of the virus do not react on cells of the subject when AB 19 was administered, it doesn't cure either".
Sai kawuna suka kara daukan zafi. Farkon bullowar annoban, masu binciken cututtuka a NDCC na rose city sunyita hada magunguna suna gwadawa suga in zasu samo maganin cutar amma ba a dace ba. Case din farko da suka fara ji ya zone daga wata mata da aka kai general hospital. Kwananta biyu a can ta mutu, lokacinda NDCC suka bada symptom na ciwon wanda bai wuce shakewaba se a mutu, suka samo case din daga hospital. Cutar a jikin matar ya dan jima kafinta shake ta mutu wanda ya tabbatar da cewa kwayoyin cutan dake jikinta a wanna lokacin be rikidaba, mutation kenan.
Amma yanzu matsalan shine, a gwaje gwajensu, sun gano cewa cutar ta rikide ta canza salo. Maganin da suka hada me karfi suka gwada akan dabbobin gwaji wato lab rats, baya aiki. Abinda yasa baya aiki, cutar ta hado wani sinadari daga jikinta dazai kareta daga maganin sannan kuma ita cutar tana harba wannan sinadari me kamada kibiya ya soke cells(kwayar halitta dake jikin dan adam wanda taruwarsu ke hada dan adam gabaki daya) na jikin dabban da ake gwaji dashi, wanda aka basu maganin da NDCC suka hada me suna AB 20, Wanda ke sanadiyan nan da nan dabbobin gwajin masu yawa suka mutu.
Cutar tana rikida da sauri cikin mintoci kadan sannan Kuma tana hada wannan sinadarin hari me yawa da karfi. Karfin maganin, karfin sinadarin. Shiyasa duka dabbobin gwajin suka mutu a kankanin lokaci. Yanzu ba karfin maganinba, hada maganin da zai iya kashe CD wato cervix disease(ciwon makoshi).
5pm
Zaune kan couch a cikin office din boss rikeda Kai, asiyace tunanin halinda dan uwanta yake ciki ya isheta. Har yanzu ba labarinshi, bata ma son zuciyarta ta aiyana mata da cewa bashi. Addu'a take tayi duk sanda tayi sallah ta kai goshinta kasa, Allah dawo dashi gida lafiya.
Cervix disease tayi illah babba ga mutanen rose city. Inta tuna gawawwakin dake kwance a kasa se hawaye kawai zataji suna gangarowa a kumatunta. Wasu mutanene masu gata, wasu basuda gatan, wasu nada masoya, wasu makiya garesu. Wasu yarane, yaushe ma suka shigo duniya gashi cutar tayi awon gaba dasu. Ga gawawwakin mata masu ciki wadanda aka nuno news basuma samu sun haifaba. Allahu Akbar, lallai Allah yayi gaskiya dayace kowane rai zata dandani zafin mutuwa.
Asiya ta mike taje balcony, ballema mutuwa cikin radadin shakewa da azaban wannan cutar. Can ta hango wata pickup na dosowa, Asiya ta matso kusada glass din balcony ta dafa tana kallon motan.
Mutane biyu sanyeda hazmat suit(tufafin kariya daga cuta mai tsananin yaduwa) suke fito daga pickup din, daya ya zagaya ta boot ya dauko wani abu dogo ya wurga kasa. Dayan mutumin ya fesa wani ruwa a jikin gawan dake kusadashi ya durkusa ya rola gawan kan ledanda dan uwan aikinshi ya riga ya bude. Suka nannade gawan tas, suka daga suka jefa boot, suka cigabada da aikin kwashen gawawwakin.
Kirrrr!!! Asiya ta daka tsalle ta dafa goshinta da hannu daya da dayan ta dafa kirjinta dake neman fashewa saboda tsoro. Ta zaro wayarta daga aljihu. BADAM!!! Kirjinta ya sake bugawa saboda lambar data gani, tayi hanzarin dauka.
"Assalamu alaikum, uncle Ahmad Kaine!?"
"Wa alaikumussalaam, eh nine yar uncle, naji ance kina pharmacy din tun safe?" Asiya ta saki ajiyan zuci, dama fargabanta kada wanine ya kira fada mata bad news.
"Hakane uncle kana gidane?"
"Alhamdulillah na dawo lafiya na iske kowa lafiya. Wake tare dake?"
"Aini kadaice anan....".
"A a, abokiyar aikinki batazo bane? Ina guard din kuma?"
Asiya tayi jim tana tunani. Muddin ta amsa da cewa ummi tazo, zai tambaya meya faru, to ita ta zauna se ita ummince zata tafi? Ummi zata iya rasa aikinta, in komai ya dawo daidai.
"Tazo, amma ina zuwa aka kirata daga gida ba lafiya, shine nace kawai taje taji kome ya faru, tunda gidansu kusane zata iya dawowa if its not serious. Guard din ma matarshi ba lafiya so i had to release him, wanda zaizo karbanshi kuma baizoba, at least i now know why he didn't show up".
"Ayyah karki damu, nasan abinda tsoro. We will get you back home Insha Allah, and thank you for staying and for awakening me with your call".
Awakening? Me uncle dinta ke nufi da hakan? Ahmed yayi mata bayanin abinda ya sameshi. Lallai wannan shine tsallake rijiya ta baya. Gama wayanta keda wuya ta bugama ummi ta sanar da ita excuse din data bata. Don kada a dawo aiki aji magana biyu. Ummi harda hawaye don tausayi ganin yanda ta tafi abinta tabar Asiya ita kadai. Amma hakan baisata kin taimakontaba, lallai Asiya mutumce. Ummi ta dauka alkawari a zucinta saita taimakawa Asiya ta isa gida Insha Allah, se inda karfinta ya kare. Ta kanta akeji, tuni Asiya, ta kusa jefarda waya wurin zumudin daukan kiran mom. "An ganshine mom?".
"Alhamdulillah gashinan....".
"Mom banishi....".
"Kyade bar.....
"Hello sis".
"Toh ashe ma ya fita zumudin", mom tanata surutunta.
"Rouk ya kake, meya sameka? Muryar Asiya ya harke.
"Hmmmm sis, ai ni naga mutuwa tana kallona ina kallonta. Kuma ko'ina na waiga itace".
* * * *
Rigan farouk sharkaf take da zufa, yana dingishi yana goge zufa da bayan hannunshi. Tafiya yakeyi cikin daji har Allah yasa yaga hanyan titi. Ya hau titi ya cigaba da tafiya. Bayan wani lokaci ya iso wani kantin saida kayan masarufi a gefen titi.
Daga gani cikin hanzari aka bar wurin donko shagon rabin kofan bude yake. Farouk ya leka hagu da dama ba mutum, sannan ya dosa shagon cikin sauri da dingishi. Farouk ji yayi kaman ya zuba ruwa kasa ya sha, ko kuma kawai yasha ruwan, don yayi tafiya kaman ba gobe. Yaci gudu harna Inna naha. Makogoronshi har wani tauri yayi saboda bushewa. Kaman ya cire boots din kafarshi ya watsar.
Isarshi shagon keda wuya ya suri bottled water, ya fincike marfin, ya kafa kai yana kwankwada. Ya sha ya Kai rabi saiya fara hango wani abu ta cikin roban ruwan daga nesa, kaman yana zuwa a guje. Haba, idanunshi suka fito a zare, da yayi watsida roban, kafa me naci ban bakiba ya arta a guje kaman wanda zaki ya biyoshi.
Mutane biyune tsaye gefen titi, daka gansu zaka tabbatarda cewa lallai sunji jiki. Budurwa da 'yar karamar yarinya suka tsaya sunata kallon bayan Farouk yanata falfalawa da gudu. Shine bai tsayaba seda ya tabbatar baya hango kowa sannan ya bar gudu. Bakin wata bishiya ya samu ya zauna yanata nishi.
"Kai Masha Allah, ashe kawai mutane masu ra....". Jikin farouk ya girgiza cikin tsoro ya kallo saman bishiya, wani saurayine makale kan reshen bishiyan yana kallon Farouk cikin farin ciki. Yana kokarin saukowa, aiko da Farouk ya lura da saurayin zai sauko, zumbur ya mike, duk gajiyan gudun da yaci dazu ya bace. Ya bar wurin kaman walkiya. "Bawan Allah....". Inaaaa yayi nisa.
Gudu yakeyi yana tara nisa tsakaninshi da mutane. Su dai sun rantse sai sun tafi lahira taredashi. Bayan abinda ya gani na tashin hankali ai shi baya fatan haduwa da kowa. Ai kila dai yanzu yayi ni.....sai Farouk ya waiga baya. Waigawanshi keda wuya mezai gani, almajirai biyu sun nannaro a guje suna a taimakesu. Eh, ai shima taimakon yake nema, daga sharrinsu.
Aiko kara taka speed yayi zuut ya bace musu. Suka tsaya suna mamakin wannan wane irin gudune dashi haka! Farouk bai tsaya ko'inaba seda yaga kanshi a zoom street. Ya jingina da wani bangon gida yana rikeda kirji yana nishi. Cikin hanzanri ya boye gefen bangon, yana tunanin idan cutan bata kashe shiba, gudu zai kasheshi.
Gawawwakin dake wurin yaga ana rolasu a leda ana turawa bayan boot din pickup. Can wuri ya kacame da karan siren na motoci. Motocin suka tsaya, sojoji sanyeda gas mask suka fito daga mota, daya na rikeda tracker. Ya nuna inda farouk ke makale.
Juyawan farouk ze gudu yaci karo da mutum ya fadi kasa. Shike nan, sun cimmishi a karshe. Rayuwarshi ta kare, gashi ko aure ma baiyiba. Yasa hannu a kai sannan ne ya lura da gas mask da uniform na soja. Da baya da baya ya farayi ya juya zaiyi rarrafe ya gudu.
"Are u Farouk liman?", sojan dayaci karoda ya tambayeshi, muryarshi a shakare saboda gas mask dayasa. Farouk ya taka birki ya juyo yana kallonshi. Canya daga Kai, eh. Sojan ya saitoshi da tranquilizer gun(bindiga mai daukeda maganin bacci), ya harboshi a wuya. Farouk ya taba wuya, ya fara ganin bibbiyu. Shike nan, mutuwan tazo..... Ya sulale ya fadi kasa, duhu ya tafi dashi. Ko mutuwance ma yanzu dai ta kam mishi.
* * * *
"Hahhhahhhahhah aha hahaha, kaiii rouk, ashe kaji jiki". Asiya tana dariya tana share hawaye.
"Hmm sis, ai farkawa kawai nayi naganni a kan gado, isolation center. Daga nanne na hango su dad. Happiness ba a iya misali. Tunda ban nuna symptoms of cervix disease ba aka sallameni. Wallahi dukda haka sis, inaji in my bones son guduwa idan naga mutane...". Asiya ta kwashe da dariya. Ta rike ciki "Oh please you are killing me, wannan gudu sai kace me gudun marathon".
Karan soye soyen abinci ke tashi daga kitchen din pharmacy. Asiya na soya doya tana hada chicken sauce. Tun breakfast din datayi, bata iya sama bakinta komaiba. Ta gama ta dauka plate ta tafi balcony na office din boss, ta zauna a kujeran data ajiye a wurin. Masu kwashe gawan nata aikinsu. Ita kam bazata iya zaman kallonsuba ballema cin abinci a gabansu, ta koma cikin office ta zauna a couch ta dauka remote ta kunna t.v dake makale a bango.
Bayan abubuwanda suka faru, Asiya taji jikinta ya mutu. bayanta na jingine da couch, fuskarta na kallon sama. Farouk ya dawo, boss dinta ma haka, ummi na gida cikin koshin lafiya. Murmushi ya sauka a lebenta, Idanuwanta sukayi nauyi. Baccin gajiya ya saceta zuwa duniyan daba mafarki.